Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya za ta amfana daga yarjejeniyar AfCTFA
2019-07-08 14:03:17        cri


A ranar Lahadi 7 ga watan nan na Yuli ne, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sanya hannu kan yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta nahiyar Afirka ko AfCTFA a takaice, yarjejeniyar da ake fatan za ta samar da zarafin kara inganta hada hadar kasuwanci tsakanin kasashen dake nahiyar, da bunkasa tattalin arzikin su, da samar da ci gaba mai dorewa.

Najeriya tare da Benin ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar, yayin taron kungiyar tarayyar Afirka ta AU da ya gudana a birnin Yamai, fadar mulkin janhuriyar Nijar, inda kuma a yayin taron, aka kaddamar da tsarin aiwatarwa na wannan yarjejeniya.

Gabanin taron na ranar Lahadi, gwamnatin Najeriya ta amince da a gudanar da bincike, da jin ra'ayin masu ruwa da tsaki, karkashin kwamitin da shugaban kasar ya kafa, wanda daga karshe ya gabatar da rahoton sa na amincewa da shiga yarjejeniyar.

Yarjejeniyar AfCFTA, daya ce daga manyan ayyukan dake kunshe cikin ajandar kungiyar AU ta nan da shekarar 2063, wadda ta tanaji samar da kasuwar bai daya ta Afirka, domin hajoji da ayyukan hidima, tare da ikon zirga zirgar mutane da kayayyaki, da ma harkokin zuba jari tsakanin kasashen nahiyar.

Masana sun ce hakan zai haifar da kafuwar yankin ciniki maras shinge mafi girma a duk duniya, wanda kasashe mambobin kungiyar AU 55 suka kirkira a watan Maris na shekarar 2018, inda da fari kasashen nahiyar 44 suka amince da kafuwar ta, kafin daga bisani Najeriya, kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar ita ma ta amince da hakan.

Mahukuntan Najeriya sun ce kafin amincewa da ita, sai da suka baiwa sassan masu ruwa da tsaki, kamar kungiyar kwadago ta kasar NLC, da kungiyar masana'antun kere kere da sauran su, damar duba alfanun shiga yarjejeniyar. Wani dalilin na daban na wannan jinkiri shi ne, duba yiwuwar shiga tsarin da zai haifar da cinikayya maras adalci, kamar jibge hajoji da ka iya jawo karyewar darajar kayayyakin da ake sarrafawa a cikin kasar. Hakan a ganin wasu manazarta na cikin kasar na iya haifarwa Najeriyar hasara, bayan sanya hannu kan yarjejeniyar. A gefe guda kuma, akwai masu ganin cewa, Najeriyar za ta yi matukar amfana daga yarjejeniyar ta AfCFTA, duba da cewa kasancewar ta a ciki, zai zaburar da hada hadar cinikayya a yankin da take.

A watan Yuni da ya gabata, jakadan kasar Masar a Najeriya Assem Hanafi, ya bayyana damuwa, game da karancin hada hadar cinikayya tsakanin Masar da Najeriya, yana mai cewa, akwai matukar bukatar fadada kasuwannin sassan biyu. Jami'in na wannan tsokaci ne, a daidai gabar da cinikayya tsakanin kasashen nahiyar ba ta wuce kaso 15 bisa dari, na jimillar cinikayyar da kasashen ke yi da takwarorin su na sassan duniya ba.

A cewar wani shaihun malami dake koyarwa a tsangayar kimiyyar siyasa da cudanyar kasa da kasa a jami'ar gwamnatin tarayyar Najeriya ta Abuja Dr. Sheriff Ghali Ibrahim, mafi yawan kasashen Afirka ba sa gudanar da cinikayya tsakanin su. Ya ce a matsayin Najeriya na kasa mafi yawan al'umma, kuma babbar kasuwa a nahiyar Afirka, tana da babbar rawa da za ta taka a fagen bunkasa hada hadar cinikayya tsakanin kasashen nahiyar.

Malamin wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce kawar da shingen cinikayya karkashin tanajin wannan yarjejeniya, zai baiwa Najeriya zarafi na tallata dumbin hajojin ta ga sauran kasashen dake nahiyar Afirka.

Malam Sheriff Ghali Ibrahim, ya ce a shekarar 2017, yawan hajojin da Najeriya ke fitarwa sauran kasashen Afirka bai wuce kaso 12 bisa dari, na hajojin da kasar ke fitarwa sassan duniya ba, kana ita ma Najeriyar na shigo da kaso 4 ne kacal daga sauran kasashen nahiyar, yayin da sauran kason ke shigowa daga sauran kasashe dake wajen nahiyar. Alkaluma sun nuna cewa, Najeriya na fitar da albarkatun man fetur ne kadai zuwa wasu kasashen Afirka. Inda Afirka ta kudu ta kasance babbar kawar Najeriyar ta fuskar cinikayya.

Ya ce kasar na shigo da kayan sinadaran roba, da takin zamani, da kayan karo, da daskararren kifi daga wasu kasashe da ba mambobin kungiyar ECOWAS ba, kuma dukkanin wadannan hajoji ana buga musu haraji. Sai dai a yanzu da yake an kawar da wannan shinge na kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar, ita ma Najeriya za ta fara cin gajiya daga kasuwar takwarorin ta dake sassan Afirka.

A nasa tsokaci kuwa, tsohon minista kuma shugaban cibiyar cinikayya da raya masana'antu da cinikayya ta birnin tarayya Abuja Adetokunbo Kayode, ya ce tsarin yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta Afirka, ba zai haifarwa Najeriya wata illa ta fuskar tattalin arziki ba. Ya ce yarjejeniyar ta yi cikakken tanaji na dakile fasa kwauri, da jibge hajoji, da ma sauran matsaloli daka iya yin tarnaki ga ci gaban daidaikun kasashen dake cikin ta.

Maimakon haifar da kalubale, Mr. Kayode na ganin AfCFTA za ta ma samarwa Najeriya da al'ummar ta, karin damammaki ne na fadada harkokin cinikayya da kasuwanci.

Daukacin sassa masu zaman kan su a tarayyar Najeriya, sun yi amannar cewa, yarjejeniyar AfCTFA, za ta karade fannonin cinikayyar hajoji, da hidimomi, da sashen zuba jari, da kuma dokoki da tsare tsare na warware sabani.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China