Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gibin dake tsakanin tunanin iyayen birane da na karkara ya ragu a Sin
2019-07-08 09:57:27        cri

Wani bincike da aka gudanar a kwanan nan ya nuna cewa, yanayin rayuwar iyalai mazauna karkara na kasar Sin ya yi matukar kyautatuwa, lamarin da ya nuna cewa, banbancin dake tsakanin tunanin iyaye mazauna birane da mazauna karkara ba shi da yawa sosai.

Cibiyar tattara bayanai ta data100.com ta gudanar da binciken, inda ta tattauna da sama da mutane 1,500 daga wasu garuruwa 172 a larduna 8 na kasar Sin.

Sakamakon binciken da aka samu na wadannan garuruwa ya nuna cewa, iyaye suna biyan kimanin yuan 1,476 kwatankwacin dala 214.8 a kowane wata wajen kulawa da 'yayan da ba su kai 'yan shekaru 3 ba, yayin da mazauna kananan birane suka kashe yuan 1,562 da kuma yuan 1,661 ga mazauna manyan biranen kasar.

Bisa la'akari da zabin da ake da su na renon kananan yara, gibin dake tsakanin iyalai mazauna birane da mazauna karkara yana raguwa sannu a hankali. Alkaluman bayanan da aka samu daga binciken sun nuna cewa, kashi 23.8% na iyaye mazauna karkara suna sanar da 'yayansu wasu labarai, wanda ya yi kasa da kashi 30% na iyaye da aka zanta da su a birane. Kuma kwatankwacin adadin littattafai da kowanen iyalin karkara ya mallaka ya kai guda 8.1, adadin da ya yi dadai da na mazauna kananan biranen kasar ta Sin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China