Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kara takaita sassan da baki ba za su zuba jari ba
2019-07-01 15:47:17        cri

Jiya Lahadi ne, gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar sassan da baki ba za su zuba jari ba ta shekarar 2019, da takardar sassan da baki ba za su zuba jari ba a fannin yankunan cinikayya cikin 'yanci na gwaji, inda aka amince da jarin waje su samu 'yancin tafiyar da harkokin wani kamfani ta hanyar mallakar wani kason hannayen jari ko gudanar da harkoki da zuba jari shi kadai. Takardar tana zuwa ne sa'o'i 48 bayan da shugaban kasar Xi Jinping ya sanar da cewa, kasarsa za ta kara bude kofa ga kasashen ketare a fannoni guda biyar a yayin taron koli na G20 da ya gudana a birnin Osaka na kasar Japan. Matakin da kasar Sin ta dauka cikin sauri ya nuna cewa, kasa ce mai karfin gudanar da harkoki.

Akwai abubuwa guda uku game da sabuwar takardar sassan da baki ba za su iya zuba jari ba. Na farko, an rage yawan ayoyin dake cikin sabuwar takardar idan aka kwatanta da takardar da ta gaba ce ta, wato yawansu a dukkan kasar Sin ya ragu daga 48 zuwa 40, kana yawansu a yankin yin ciniki cikin 'yanci ya ragu daga 45 zuwa 37. Na biyu, an bude kofa ga kasashen waje a fannoni daban daban ciki har da aikin noma, hakar ma'adinai, kera kayayyaki, sufuri, karin harkokin sadarwa, ayyukan more rayuwa, al'adu da sauransu. Na uku, a ci gaba da ba da iznin fadada bude kofa ga kasashen waje a yankin yin ciniki cikin 'yanci, kamar soke kayyade yin amfani da jarin waje a fannonin kamun kifi da buga littattafai a yankin. Sin ta yi amfani da matakan fadada bude kofa ga kasashen waje wajen kwantar da hankalin kamfanonin kasashen waje dake kasar Sin, hakan ya ba da sabuwar gudummawa kan raya hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya a fannin samar da kayayyaki.

A 'yan shekarun nan, kasar Sin tana kara zurfafa yin kwaskwarima a gida da kara bude kofarta ga kasashen ketare, tare kuma da rage wasu sassan kasuwancin da baki 'yan kasuwa ba za su iya zuba jari ba, har ma kasar za ta kawar da duk wasu abubuwa dake kawo cikas a baya ga takardar sassan kasuwancin da baki 'yan kasuwa ba za su iya zuba jari ba. Alal misali, an rage adadin sassan kasuwancin da baki 'yan kasuwa ba za su iya zuba jari ba a yankin cinikayya maras shinge na Shanghai daga 190 a da zuwa 37 a yanzu. Har wa yau, a watan Maris din bana, gwamnatin kasar Sin ta zartas da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, wadda ta ayyana wasu ka'idoji na musamman kan 'yancin mallakar fasaha na kamfanonin jarin waje, da yadda za su iya zuba jari da samun moriya da sauran wasu halaltattun hakkokinsu a kasar ta Sin.

Hakika, ya zama tilas ga kasar Sin wadda ke neman samun ci gaba mai kyau tare da kara kawo wa jama'ar kasar alheri ta kara bude kofa ga kasashen ketare. Bisa tanade-tanaden da ke cikin sabuwar takardar, nan ba da dadewa ba za a sassauta ko soke yadda aka takaitawa 'yan kasuwan waje zuba jari a fannonin gidajen sinima, hukumomin kula da wasannin fasaha da sauran sassan ba da hidima. Lamarin da zai taimaka wajen daga matsayin ci gaban masana'antun kasar Sin, kara azama kan kamfanonin Sin da su kara karfinsu na yin takara, da kara sanya jama'a jin dadin zamansu na rayuwa.

Sabuwar takardar za ta habaka sabbin fannonin da 'yan kasuwan ketare za su zuba jari a kai. Yanzu haka kusan 'yan kasuwan waje na yin kusan rabin cinikin waje a nan kasar Sin, tare da samar da ribar da yawanta ya kai kusan kashi 1 cikin kashi 4 na jimilar ribar da manyan masana'antun kera kaya suka samar a kasar ta Sin. Alal misali, a wannan karo, an yarda masu jarin waje su yi mallaki gidajen sinima da hukumar kula da wasannin fasaha. Ko shakka babu dukkan 'yan kasuwan waje za su nuna sha'awarsu kan babbar kasuwar kasar Sin mai yawan mutane biliyan 1.4, inda ake samun kudin tikitin kallon sinima da yawansa ya kai kusan biliyan 60 baki daya.

Tun farkon wannan shekarar da muke ciki, takaddamar dake tsakanin Sin da Amurka na kara tsananata, aikin da ya kawo babbar illa ga tsarin sana'o'i na duniya, da tsarin moriyar kasa da kasa da tsarin samar da kayayyaki, a matsayin kasa mafiya girma ta fuskar cinikin kayayyaki, da kasar dake kai matsayin biyu a fannin ba da hidimma, yadda za ta kwantar da hankulan kasa da kasa a cikin yanayin maras tabbaci, ya zama muhimmin aiki ne, kuma ya jawo hankalin kasa da kasa kwarai da gaske.

Kamfanonin kasashen waje da dama sun mai da kasuwar kasar Sin a matsayin ginshiki mai muhimmanci wajen goyon bayan tsare-tsarensu na samun bunkasuwa a duk fadin duniya, wannan ya sa su kara zuba jari a kasar Sin. Ban da kafa babbar masana'anta da kamfanin kera motoci na Tesla da Amurka ke yi a birnin Shanghai, kamfanin sadarwa na Telecom na kasar Birtaniya shi ma ya zama kamfanin sadarwa na farko a duniya da ya samu iznin tafiyar da ayyukansa a kasar Sin. Ban da wannan kuma, kamfanin inshora na Allianz shi ma ya samu iznin kafa kamfanin inshora na farko mai jarin waje a Sin, baya ga yadda Sin ta amince da kamfanin Standard & Poor's ya tantance ingancin kasuwarta wajen biyan bashi.

Yadda aka takaita sassan da 'yan kasuwa baki ba za su zuba jari ba a kasar Sin, ya nuna wa duniya cewa, kasar tana kokarin bude kofarta ga kasashen waje, haka kuma ya zama wata manufar da za ta tabbatar da 'yancin kamfanonin kasashen waje na zuba jari a kasuwannin kasar Sin, da samun damammakin raya kansu, da amfanawa dukkan bangarori.

Abubuwan da suka faru a zahiri sun shaida cewa, duk da sauyin yanayi da ake fuskanta a duniya, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da bunkasa kamar yadda ake bukata. Sa'an nan kasar na son rungumar duk wani abokin hulda, bisa ra'ayi na tattaunawa, da raya harkoki tare, gami da samun moriya tare. Kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a kokarin dunkulewar duniya waje guda, kana kasar Sin abokiyar hulda ce da za a iya dogaro a kanta. (Bilkisu, Zainab, Murtala, Amina, Tasallah, Kande, Bello)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China