Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkibla da babban aikin 'yan jami'yyar kwaminis ta kasar Sin
2019-07-01 14:17:35        cri

 


Yau ranar 1 ga watan Yuli, ake cika shekaru 98 da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ko kuma JKS a takaice. A farko dai, babu yawan mabiyanta, amma a cikin wadannan shekaru 98, yawan mambobinta ya karu zuwa miliyan 90, har ta zama jam'iyya mafi girma a duniya. Jam'iyyar ta jagoranci jama'ar kasar Sin don su magance matsaloli da mawuyancin hali iri daban-daban da samun wasu nasarori masu ban mamaki, ba tare da la'akari da tana da karfi ko ba ta da shi ba, ko tana cikin yanayi mai kyau ko mara kyau ba. Me ya sa jam'iyyar ta iya samu irin wadannan nasarori? To, bari mu saurari yadda shugaba Xi Jinping ya yi bayani kan wannan tambaya, da kuma alkibla gami da babban aiki na 'yan JKS.

Yanayin kaka na shekarar 2017, mako daya bayan an kawo karshen babban taron JKS karo na 19. Shugabannin kasar Sin da suka kama aikinsu ba da dadewa ba a wancan lokaci sun kai ziyara birnin Jiaxing na lardin Zhejiang, don waiwayen tarihin kafuwar jam'iyyar. Zaunannun mambobin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin sun tashi daga birnin Beijing suka kai ziyara wani wuri tare, aikin da ba a kullum ake ganin irinsa ba, a cikin wannan aiki dai, shugaba Xi ya yi kira ga daukacin jam'iyyar cewa, kada a manta da alkiblar JKS da nacewa ga babban aikin da tilas su yi. To mene ne alkibla da babban aikin 'yan JKS? A cikin rahoton da aka gabatar a babban taron, shugaba Xi ya bayyana cewa:  

"Alkibla da babban aikin 'yan JKS shi ne samarwa jama'ar kasar rayuwa mai inganci da farfado da al'ummar Sinawa. Wannan alkibla da babban aiki ya karawa 'yan JKS kwarin gwiwa don samun ci gaba. Kamata ya yi, 'yan JKS su maida aikin gyara zamantakewar al'umma a gaban komai da kokarin cimma wannan muradu. Kuma kada a tsaya a kan hanyar farfado da al'ummar Sinawa da yin iyakacin kokari cimma wannan muradu."

Mai da burin jama'a gaban komai babban tunani ne dake cikin matakan da shugaba Xi yake dauka kan mulkin kasa da tafiyar da harkokin kasa. Tun lokacin babban taro karo na 18 na JKS, an dauki jerin matakai na yiwa wasu tsare-tsare gyaran fuska, yawancinsu na da alaka da zamantakewar jama'a. Daga cikinsu, yadda za a fitar da matalauta daga talauci ya fi jan hankalin shugaba Xi. Hakan ya sa, shugaba Xi ya kai ziyara wurare 14 da suka fi fama da talauci a kasar Sin a cikin wadannan shekaru da suka gabata.

JKS jam'iyya ce dake mai da muhimmanci sosai kan zamantakewar Sinawa, har ta taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da Bil Adama gaba. A gun taron koli tsakani JKS da jam'iyyun siyasa daban-daban na kasa da kasa, shugaba Xi ya bayyanawa shugabannin jam'iyya da na kungiyoyin siyasa kimanin 300 daga kasashe daban-daban cewa, JKS na fatan kara tuntubar sauran jam'iyyun kasa da kasa don more kimiyyar tafiyar harkokin kasa da yin musanyar ra'ayi, kana da kara amincewa da juna , da kuma sa kaimi ga kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkanin Bil Adama, har ma da raya duniya cikin hadin kai. Ya ce:

"Duk wani aikin da JKS yake yi na da zummar kyautata zamantakewar al'ummar Sinawa, da farfado da al'ummar Sinawa, kana da neman shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya. JKS ta kafu ne bisa tushen jama'a, kuma tana samun bunkasuwa ne ta hanyar dogaro da jama'a, hakan ya sa take kokarin samarwa jama'ar Sin har ma jama'ar dukkanin duniya rayuwa mai inganci."(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China