Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Barazanar kara sanyawa Sin haraji ba za ta iya warware matsala ba
2019-06-27 20:26:54        cri

Ana sa ran shugabannin kasashen Sin da Amurka za su gana da juna a yayin taron koli na Osaka na kungiyar G20. Amma a wannan lokaci, bangaren Amurka ya sake yin barazana kan cewa, wai Amurka za ta kara sanyawa kasar Sin haraji, idan har sassan biyu ba su cimma yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya ba. Gaskiya, wannan furucin ya saba ra'ayin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, wanda kuma bai dace da hirar da shugabannin biyu suka yi ta waya a kwanan nan ba. Lamarin da ba zai taimaka wajen warware matsala ba.

Matsayin Sin a kan warware takaddamar cinikayya a tsakaninta da Amurka bai canja ba ko kadan, wato tattaunawa da juna cikin daidaito, da lura da batutuwan da bangarorin biyu suka mayar da hankali a kai. A cikin shekara guda da ta wuce, kasar Sin ta nuna matukar sahihanci wajen yin shawarwari har karo 11 tare da Amurka, kuma duk an samu babban ci gaba. Amma Amurka ta ci amanarta har sau uku, inda take ta kara sanyawa Sin haraji, lamarin da ya kawo cikas ga shawarwarin matuka.

Ana iya lura cewa, kafin a bude taron koli na Osaka na kungiyar G20, kasar Japan ta bayar da takardar bayanin cinikayya ta shekarar 2019, inda ta yi gargadi kan ra'ayin ba da kariyar ciniki da ke kara tsananta a kasar, kuma ta nuna cewa, yawan matakan kawo tarnaki ga cinikayya zai hana karuwar tattalin arzikin duniya, don haka ta yi kira ga kasashen da abin ya shafa da suka yi hakuri a kan batun. A hakika dai, wannan shi ne ra'ayin yawancin kasashe membobin kungiyar G20. Kada a manta da batun tinkarar raguwar cinikin duniya da kashi 60 cikin dari da koma bayan tattalin arzikin duniya tun bayan da Amurka ta zartas da dokar Smoot-Hawely a shekaru 1930 na karnin da ya gabata. A halin yanzu, kasar Amurka ta dauki matakan kara sanya haraji don kawo illa ga kasashe membobin kungiyar G20. Ya kamata a dora muhimmanci ga ra'ayin bangarori daban daban, da yaki da ra'ayin bangare daya, da nuna goyon baya ga ra'ayin bude kofa ga kasashen waje da yaki da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya a gun taron kolin Osaka a wannan karo.

A matsayinta na kasa dake daukar alhakinta, kasar Sin za ta duba batun tattalin arziki da cinikayya a tsakaninta da kasar Amurka cikin adalci don tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya da moriyar jama'arsu. Amma Sin ba ta jin tsoron matsin lamba ko barazana da aka yi mata, ta riga ta shirya tinkarar duk wani irin kalubale. Idan Sin da Amurka suna son cimma yarjejeniya, ya kamata su yi shawarwari cikin adalci. Matakan kara sanya haraji ba su da wani amfani ga kasar Sin. Idan Sin da Amurka suka yi hadin gwiwa cikin sahihanci, to. za a warware matsalar tattalin arziki da cinikaya a tsakaninsu.(Kande, Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China