Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin kan moriyar juna tsakanin Sin da Afirka zai taimakawa ci gaban duniya
2019-06-26 19:23:52        cri

Ana gudanar da taron masu shiga tsakani kan aikin tabbatar da nasarorin da aka cimma a yayin taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar murnar bude taron, inda yake sa ran cewa, sassan biyu wato Sin da Afirka za su yi kokari tare bisa ka'idar moriyar juna domin gina kyakkyawar makoma ga al'ummun Sin da Afirka ta hanyar gudanar da tattaunawa a tsakaninsu. Kana tun daga Alhamis dake tafe, za a kaddamar da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na farko a Changsha, babban birnin lardin Hunan na kasar Sin, makasudin shirya bikin shi ne domin tattauna matakan yadda za a ingiza hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu a bangarorin tattalin arziki da cinikayya.

A watan Satumban bara ne, aka kammala taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka cikin nasara, taron da yake da babbar ma'ana a tarihin cudanyar dake tsakanin sassan biyu. Yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da hada kai tare da kasashen Afirka domin gina kyakkyawar makoma ga al'ummun Sin da Afirka, kana za ta kara mai da hankali kan shirye-shirye guda takwas da aka tsara yayin da take gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka, shirye-shiryen sun shafi bangarorin raya sana'o'i, da cinikayya, da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kara karfin tafiyar da harkokin kasa, da kiwon lafiya, da cudanyar al'adu, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Yanzu haka an riga an tsara hakikanan shirye-shirye, lokaci kawai ake jira na fara daukar hakikanan matakai, har kullum kasar Sin tana cika alkawarin da ta dauka, shi ya sa aka shirya taron masu shiga tsakanin domin tabbatar da matsayar da shugabannin sassan biyu suka cimma.

Hakika hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu ya riga ya samu ci gaba a bayyane tun bayan da aka kammala taron kolin Beijing a bara, misali an kammala taron tattaunawa kan zaman lafiya na Sin da Afirka cikin nasara, kana kasar Sin ta kafa cibiyar nazarin harkokin kasashen Afirka, ban da haka kuma kasar Sin da kasashen Afirka sun riga sun tsai da kuduri cewa, za su aiwatar da ayyukan hadin gwiwa da yawansu zai kai sama da 880 cikin shekaru 3 masu zuwa, duk wadannan sun shaida cewa, ana gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka cikin lumana, haka kuma hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu tana da makoma mai haske.

Ingantuwar hadin kan Sin da Afirka ba ma kawai ta biya bukatun junansu ba, har ma ta dace da sauye-sauyen da duniya ke fuskanta. Da farko dai, yadda Sin da Afirka ke kyautata hadin kansu ya dace da ka'idar moriyar juna da samun nasara tare. Darajar cinikayyarsu ta kai dala biliyan 204.2 a bara, wadda ta karu da kashi 20 cikin dari bisa na shekarar 2017. Ban da wannan kuma, Sin ta zama abokiyar cinikin Afirka mafi girma a duk duniya a jerin shekaru 10 da suka gabata. Kawo yanzu dai, kasashen Afirka 40 da kwamitin kula da harkokin kungiyar AU sun riga sun daddale yarjejeniyar hadin kai tare da Sin bisa shawarar "ziri daya da hanya daya". Wasu ayyuka kamar layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobin Kenya, da yankin hadin kan tattalin arziki da ciniki na Suez na kasar Masar na taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasashen Afirka.

A sabo da haka, a dangane da zargin da ake yi wa Sin kan cewa wai Sin na saka wa kasashen Afirka tarkon bashi, shugabannin Kenya da Ruwanda da dai sauransu sun musunta. Inda shugaban kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni ya bayyana a ranar 25 ga wata a Beijing, cewar Sin da Afirka aminai ne. Kasar Sin ta ba da babban taimako, yayin da al'ummar Afirka ke kokarin neman 'yancin kansu da raya kasashensu, Afirka na son koyon fasahohin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin na gudanar da harkokin kasa.

Ban da wannan kuma, Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, yayin da Afirka nahiya ce da ke da yawan kasashe masu tasowa, yawan al'ummar bangarorin biyu ya kai kashi 34 cikin dari na al'ummar duniya. Don haka, yadda duniya za ta kasance a nan gaba ya danganta da makomar ci gaban Sin da Afirka, hadin kan Sin da Afirka na da babbar ma'ana ga duk duniya. A wani bangare, yanzu ra'ayin bangaranci da na ba da kariyar cinikayya na addabar duniya, Sin da Afirka dukkansu na fatan hadin gwiwa don kiyaye tsarin kasancewar bangarori da dama.

'Yan siyasa na kasashen Afirka kamar Yoweri Kaguta Museveni da sauransu sun yi nuni da cewa, ra'ayin bangare daya hadari ne, ya kamata Afirka da Sin su kara yin mu'amala da hadin gwiwa kan harkokin bangarori daban daban kamar MDD da sauransu. Kana Sin da kasashen Afirka suna cikin muhimmin matakin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a, bangarorin biyu suna da burin samun bunkasuwa iri daya, ya kamata su kara yin imani da juna kan harkokin siyasa, da yin mu'amala da juna kan tafiyar da harkokin kasa, da yin hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa, hakan zai taimaka musu wajen gyara kuskure da tinkarar kalubale iri iri tare.

A halin yanzu, kungiyar AU ta tsara ajendar samun ci gaba nan da shekarar 2063, inda aka gina yankin yin ciniki cikin 'yanci dake shafar kasashe fiye da 50 na Afirka, akwai kyakkyawar makoma wajen raya kasashen Afirka. Bisa wannan yanayi, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta hada da manufofin kungiyar AU na kasashen Afirka, da kuma ajendar samun bunkasuwa mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030, hakan zai taimaka ga bunkasa sabbin kasashen kasuwanci, kuma zai yi babban tasiri ga cimma burin kawar da talauci da farfado da tattalin arzikin duniya.

Duk da sauye-sauye da duniya ke fuskanta, kasashe masu tasowa sun samu ci gaba sosai.

Sin da Afirka suna hadin gwiwa da juna, hakan zai samar da muhimmiyar gudummawa wajen kara karfin kasashe masu tasowa, da kafa sabuwar dangantakar tsakanin kasashen duniya, da raya kyakkyawar makoma ga daukacin bil Adama. Don haka, neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka zai kawo wa jama'arsu moriya, kana abu mai muhimmanci da dukkan duniya ke bukata a halin yanzu. (Jamila, Kande, Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China