Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jirgin ruwa na "The Empress of China" ya alamta cewa, ba a iya raba kasashen Sin da Amurka ba
2019-06-24 15:54:09        cri

Sakamakon tsanantar takaddamar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Amurka, wasu mutanen Amurka, kamar Marco Rubio, dan majalisar dattawa na jam'iyyar Republican na Amurka na ganin cewa, ya kamata a "raba kasar Amurka da kasar Sin", har ma sun ce, za a yanke huldar tattalin arziki da cinikayya, da ta kimiyya da fasaha, da kuma ta ilmin zaman al'umma dake kasancewa tsakanin kasashen biyu. Wadanda suke da irin wannan ra'ayi, kwata kwata sun manta da tarihi ne game da yadda kasar Amurka ta samu ci gaba. Sun manta kaka da kakaninsu sun samu arziki, har ma sun bunkasa kasar Amurka ta yau bayan da suka zo kasar Sin suka yi cinikayya da 'yan kasuwa na kasar Sin a tarihi.

A shekarar 1784, lokacin da kasar Amurka ba ta dade da samun 'yancin kanta ba, tana neman karya takunkumin da kasar Birtaniya ta saka mata. Saboda haka, a ranar 22 ga watan Fabrairu na wancan shekara, wato rana daya da ranar haihuwar George Washington, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen neman 'yancin kan kasar Amurka, kasar ta tura wani jirgin ruwan kasuwanci mai taken "The Empress of China" wato "Sarauniyar kasar Sin", don ya tafi kasar Sin ciniki. Bayan ya kwashe rabin shekara yana tafiya a cikin teku, jirgin ruwan ya isa birnin Guangzhou na kasar Sin a ranar 28 ga watan Agustan shekarar 1784, inda ya kaddamar da ciniki a karon farko tsakanin kasashen Sin da Amurka, wadanda ke kasancewa a gabobi 2 na tekun Pasific. Jirgin "Sarauniyar Sin" ya tsaya a Guangzhou har fiye da watanni 3, inda 'yan kasuwa Amurkawa dake cikin jirgin sun sayar da barkono da auduga, da sauran kayayyakin da ake samarwa daga Amurka, tare da sayen abin shayi na Tea, da kayayyakin fadi-ka-mutu na kasar Sin. Ta wannan ciniki, 'yan kasuwar sun samu ribar da darajarta ta kai fiye da dalar Amurka dubu 30.

Wannan doguwar tafiya mai ma'ana da Amurkawa suka yi kan ruwa, ta sanya su gano babbar ribar da za su iya samu a kasuwannin kasar Sin mai nisa. Ta haka 'yan kasuwan Amurka masu yawa sun tashi zuwa kasar Sin, sun kama hanyar siliki irin ta Amurka kan ruwa don yin ciniki da kasar Sin kai tsaye.

Amurka ta samu nasarar ratsa shingayen tattalin arziki da kasar Birtaniya ta sanya mata, ta kama hanyar samun ci gaba da wadata ta hanyar yin ciniki da kasar Sin cikin adalci domin samun moriyar juna yau shekaru fiye da dari 2 da suka wuce. Yau a matsayinsu na wadanda suke kan gaba a duniya ta fuskar ci gaban tattalin arziki, kasashen Sin da Amurka sun zamewa juna kasa mafi girma wajen yin ciniki da kuma muhimmiyar kasa ce ta fuskar zuba jari. Da wuya ne a yi zaton cewa, mene ne za a iya raba Sin da Amurka, wadanda suke dogaro da juna sosai.

A 'yan kwanakin nan, kamfanonin Amurka fiye da 600 ciki har da WalMart Inc. sun hada kai wajen mika wasika ga gwamnatin Amurka, inda suka bukaci ta warware takaddamar cinikayya dake tsakaninta da kasar Sin, kuma sun nuna cewa, kara bugawa kayayyakin Sin kudin haraji zai kawo illa ga muradun kamfanonin Amurka da ma masu sayayya na kasar. A yayin taron sauraron ra'ayi da Amurka ta kira kan batun kara buga haraji ga kayayyakin Sin masu dajarar Dala biliyan 300, wakilan kamfanoni da kungiyoyin sana'o'in Amurka sun nuna rashin yarda da batun, a ganinsu, babu wanda ke iya maye gurbin kayayyakin Sin, tattalin arzikin Sin da Amuka a hade suke yanzu, inda Amurka ta kara bugewa kayan Sin kudin haraji, to masu sayayyar Amurka su ne wadanda suka fi gamuwa da asara daga ciki.

A halin yanzu dai, ana gudanar da harkokin tattalin arziki a duk fadin duniya, cinikayyar Amurka da Sin ba ma kawai tana da alaka da moriyar kasashen biyu ba ne, har ma tana kawo amfani ga sana'o'i daban-daban, da tsarin sufurin kayayyaki da tsarin samun moriya. Katse huldar Sin da Amurka zai kawo illa ga tsarin tattalin arizkin duniya, har ma zai lahanta ayyuka daban daban da ake rarrabawa masana'antu daban daban na kasashen duniya, kana da haddasa girgiza a kasuwannin duniya da tada zaune tsaye a kasuwar hada-hadar kudin duniya. Game da wannan batu, tsohuwar mataimakiya mai bada shawara ga ministan harkokin waje na kasar Amurka Susan L. Shirk ta nuna cewa, maganar wai katse huldar Sin da Amurka wani babban kuskure ne, wadda za ta kawo babbar illa ga tattalin arzikin duniya, a maimakon haka, hadewar tattalin arzikin kasashen biyu ya kasance tushe mai inganci ga aikin gudanar da harkoki tsakanin kasashe daban-daban.

Ana gudanar da gagarumar cinikayya a tsakanin kasashen Sin da Amurka, don haka ba abun mamaki ba ne ake tayar da takaddamar cinikayya a tsakaninsu, abin da ya fi muhimmanci wajen tinkarar takaddamar shi ne, nemo wata hanyar da ta dace don sarrafa bambancin dake kasancewa a tsakaninsu, da kuma kara habaka ra'ayin bai daya da suka samu. Idan aka waiwayi tarihin soma cinikayya a tsakanin kasashen biyu da jirgin ruwan na "The Empress of China" ya yi a shekaru sama da 230 da suka wuce, aka gane cewa, kara sanya haraji ba zai iya warware matsala ba, a maimakon haka zai kara tsananta matsala. Maganar "katse hulda" a fannin cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, ra'ayi ne mai hadari, kuma rashin daukar nauyi ne. Sai dai kasashen biyu su tsaya kan nuna girmama juna, da nuna zaman daidaito da nema moriyar bai daya, kana da kawar da bambanci a tsakaninsu yadda ya kamata, hakan zai dace da moriyarsu.

Kada a manta, a yayin da aka yiwa Amurka kangiya ta fannin tattalin arziki, Sinawa ne suka samar da taimakonsu. Amma a yayin da yau kasar Sin ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya a kokarin inganta hadin gwiwar tattalin arzikin duniya, wasu mutanen Amurka sun manta da daga ina ne suka fito, har ta ce, neman kulla kawance a tsakanin wasu kasashen shiyyar ne ya sa kasar Sin ta gabatar da "ziri daya da hanya daya". Kamar yadda masanin ilmin tarihi na kasar Jamus Freidrich List ya fada, bayan da wani ya hau kolin wani tsauni, zai jefar matakalar da ya yi amfani da shi, don kada a bi bayansa.

Ko da yake wasu mutanen Amurka sun nuna goyon baya ga ra'ayin yanke huldar dake tsakanin Sin da Amurka, amma tarihi da hahikanin yanayin da ake ciki yanzu sun shaida cewa, Sin da Amurka za su samu moriya idan suka yi hadin gwiwa, kana za su samu hasara idan suka yi yaki da juna. Ga kasar Amurka dake fuskantar matsalar rashin tabbaci kan manufofin kasar, akwai bukatar maimaita tarihin cinikayyar waje a kasar, ta hakan za ta gano cewa, idan ta yanke hulda da kasar Sin, za ta rasa damar samun ci gaba da makoma, har ma za ta yanke hulda dake tsakaninta da duk duniya. (Sanusi, Bello, Tasallah, Kande, Amina, Bilkisu, Lubabatu, Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China