Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba a iya gane wasan da Marco Rubio yake yi ba
2019-06-19 13:48:15        cri

Bisa labarin da kamfanin Reuters ya bayar a jiya Talata, an ce, a ranar 17 ga wata, Marco Rubio, dan majalisar dattawan kasar Amurka ya gabatar da wani daftarin doka, inda ya nemi a gyara fuskar dokar mika ikon tsaron kasar Amurka, wato NDAA, ta yadda za a hana kamfanin Huawei na kasar Sin yin amfani da kotun Amurka wajen neman kudi daga kamfanonin kasar wadanda ke amfani da 'yancinsa na mallakar fasaha.

Wannan labarin da kamfanin Reuters ya bayar, ya girgiza al'ummun duniya sosai, ciki har da na kasar Amurka. An yi mamaki cewa, a matsayin dan majalisar dattawan kasar Amurka, wadda a kullum take yabawa kanta wajen kare 'yancin mallakar fasaha, ya nemi a gyara fuskar doka a fili, domin hana kamfanonin sauran kasashen duniya da su kare halaltaccen iko bisa dokokin Amurka, wannan ba son fashin 'yancin mallakar fasaha na sauran kasashen duniya ba ne? Yana neman kamfanonin sauran kasashen duniya wadanda suka yi amfani da 'yancin mallakar fasaha na kamfanonin kasar Amurka su biya kudi ga kamfanonin, amma kuma bai yarda su nemi kudi daga kamfanonin kasar Amurka wadanda suka yi amfani da 'yancinsu na mallakar fasaha ba. hakika, irin wannan mataki da ya dauka, ya sa ya zama tamkar wani dan iska da ya kan yi babakere, da ba ya son bin doka.

A matsayin mai tsattsaurar ra'ayi mafi tsanani dake adawa da kasar Sin daga jam'iyyar Republican, Marco Rubio ya kan zargi kasar Sin da satar 'yancin mallakar fasahar Amurka, har ma a kullum ya kan ce, kasar Sin na kawo barzana ga tsaron kasar Amurka. Amma a lokacin da kamfanin Huawei na kasar Sin ya kare ikonsa bisa dokokin kasar Amurka, ya nemi kamfanin sadarwa na Verizon na kasar da ya biya kudi dala biliyan 1 ko fiye, domin ya yi amfani da fasahohi fiye da 230 da kamfanin Huawei ya kirkiro da kansa, Rubio ya manta da zargin da ya kan nuna wa kasar Sin, inda ya canja matsayinsa, ya ce, kamfanin Huawei shi ne ya kasance kamar "dan iska wajen kare ikon mallakar fasaha", har ma ya nemi a gyara fuskar doka nan da nan domin hana kamfanin Huawei ya nemi kudin yin amfani da 'yancinsa na mallakar fasaha daga kamfanonin kasar Amurka. Lalle a bayyane yake cewa, Marco Rubio ya yi amfani da ma'auni iri biyu kan batun 'yancin mallakar fasaha, wato, idan kamfanonin sauran kasashen duniya suka yi amfani da 'yancin mallakar fasaha na kasar Amurka, ya kan dora muhimmanci sosai ga kasar Amurka wajen kare 'yancin mallakar fasaha. Amma idan kamfanonin kasar Amurka sun yi amfani da 'yancin mallakar fasaha na sauran kasashen duniya, to nan da nan zai canja fuskarsa ya ki biyan irin kudi, yanzu a idonsa, akwai moriyar siyasa.

A hakika dai, a idon mutane kamar Marco Rubio, batun kare 'yancin malalkar fasaha ya kasance kamar wani kayan aiki kawai. Dole ne su kansu su yanke shawarar "a yaushe, kuma yaya za a yi amfani da shi". Marco Rubio ya gabatar da daftarinsa ba tare da kowace hujja ba, ya sake kawo illa ga sunan kasar Amurka. Sabo da matakinsa ya shaida wa duk duniya cewa, a kullum kasar Amurka tana amfani da ma'auni iri biyu wajen batun kare 'yancin mallakar fasaha.

A kullum, Marco Rubio ya kan zargi kasar Sin kan wasu batutuwa. Sabo da haka, jaridar "Washington Post" ta Amurka ta siffanta cewa, Marco Rubio shi ne "daya daga cikin 'yan siyasa na gwamnatin kasar Amurka wadanda su kan zargi kasar Sin."

Mai yiyuwa Marco Rubio, mai shekaru 48 yana namijin kokarin zama irin wannan mutumin. A matsayin wani sabon tauraron dan siyasa na jam'iyyar Republican, ba tsattaurar ra'ayi kan harkokin siyasa kadai yake da shi ba, har ma ya kan nuna adawa da kasar Sin.

Amma, masu sanin ya kamata na ganin cewa, a hakika dai irin wannan wasa maras wayo da Rubio ya yi, yana bata sunan kasar Amurka. Irin wadannan mutane suna lalata moriyar al'ummar Amurka domin biyan moriyasu kawai. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China