Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kara haraji kan kayayyakin kasar Sin zai haifar da matsaloli ga zaman rayuwar Amurkawa
2019-06-18 14:15:14        cri

Daga jiya Litinin, ofishin wakili mai kula da batun ciniki na kasar Amurka ya fara gudanar da wani taro na sauraron ra'ayoyin jama'a na kwanaki 7, don neman shawarwari dangane da manufar kasar Amurka ta karbar karin haraji kan kayayyakin kasar Sin da ake shigo da su cikin Amurka wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 300. Inda a ranar farko da ake yin wannan taron, wakilan kungiyoyin sana'o'i daban daban na kasar Amurka sun bayyana kin amincewarsu kan manufar karbar karin haraji.

Masu halartar taron sauraron ra'ayoyin jama'a suna wakiltar kungiyoyin sana'o'i 324 na kasar Amurka, wadanda suka shafi dukkan fannoni na zaman rayuwar jama'ar kasar ta yau da kullum, misali kayan sutura, na'urorin ban ruwa, kayayyakin yara, kayan latironi, da makamantansu.

Kerry Stackpole, shi ne shugaban kungiyar masu samar da kayayyakin famfo ta kasa da kasa, wadda mambobinta suke samar da kashi 90% na kayayyakin famfo da ake bukata a kasar Amurka. A madadin wadannan kamfanonin, Mista Stackpole ya bukaci gwamnatin kasar Amurka da ta soke karbar karin haraji kan kayayyakin kasar Sin. A cewarsa,

"Idan aka duba wakilan da suka halarci wannan taron, suna wakiltar dimbin sana'o'i da kayayyaki iri-iri ne. Ta wannan za a iya ganin tasirin karbar karin haraji, domin dukkansu suna fuskantar matsin lamba sakamakon manufar. Nau'ikan kayayyakin da manufar ta shafa sun yi yawa, don haka tabbas ne manufar za ta yi illa ga jama'a masu sayen kayayyaki, musamman ma ta la'akari da yawan karin haraji da ya kai kashi 25%."

A nasa bangare, Bradley Mattarocci, mataimakin shugaban kamfanin Baby Trend, mai samar da kujerun yara da ake sanyawa mota, ya fadi ra'ayinsa cewa,

"Masu sayen kayayyakin yara suna lura da farashin kaya sosai. A kasar Amurka, da sauran kasashe daban daban, iyalai da yawa suna dogaro kan albashin da ake bayarwa a duk wata. Idan an kara farashin kaya, misali, farashin wata kujera shi ne dala 100, wanda ya riga ya yi yawa, yanzu sai a karu da dala 15, to, watakila za a daina sayen kayan. Za su nemi tsohuwar kujerar da aka taba amfani da ita, duk da cewa mai yiwuwa ne kujerar ta zama tsohon yayi, ko kuma ta riga ta wuce wa'adin tabbatar da inganci."

Ko da yake wakilai masu halartar taron na sauraron ra'ayoyin jama'a suna wakilar sana'o'i daban daban, amma da yawa daga cikinsu na ganin cewa, ba za a iya maye gurbin kayayyakin kirar kasar Sin ba. Saboda bayan da kasashen Sin da Amurka suka kwashe shekaru da yawa suna kokarin hadin gwiwa da juna, tattalin arzikinsu sun zama a hade suke. Kamfanonin kasar Amurka suna bukatar kayayyaki masu inganci da ma'aikatun kasar Sin ke samar musu. Mista Mattarocci ya kara da cewa,

"Kayayyakin karafa, kamfanoni masu samar da kaya, fasahar dinkin kaya mai sarkakiya, duk wadannan abubuwan da ake bukata wajen samar da gadon jarirai na tafi-da-gidanka, ba za mu same su a sauran wurare ba idan ba kasar Sin ba. Mun gwada wata dabara ta daban, amma akwai wuya matuka. Ka san kamfaninmu na da wani tarihi na shekaru 31. Cikin wadannan shekaru 31, muna samar da kayayyakinmu a kasar Sin. Sa'an nan muna maida hankali sosai kan tsaron kayanmu. Yanzu za a bukaci shekaru da yawa, kafin a iya kafa wani sabon tsari na samar da kaya, domin za mu horar da ma'aikata, da masu sarrafa injuna, da makamantansu. "

Tun daga watan Mayun bara, ofishin wakilin ciniki na kasar Amurka ya riga ya gudanar da taruka guda 4 domin sauraron ra'ayoyin jama'ar kasar game da manufar karbar karin haraji kan kayayyakin kirar kasar Sin. Mista Mattarocci ya ce, ya yi kokarin musayar ra'ayi da kamfanoni, da kungiyoyin sana'o'i, da majalisun kasar Amurka, da gwamnatin kasar, cikin shekarar da ta wuce, don neman a hana aiwatar da manufar karbar karin harajin. Aikin ya yi masa wuya, in ji shi, amma yanayin da kamfaninsa ke ciki shi ne mafi wuya, sakamakon manufar da gwamnatin Amurka ke aiwatarwa ta karbar karin haraji kan kayayyakin Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China