Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bada shawarar jagorantar samun ci gaba a Turai da Asiya
2019-06-11 14:09:01        cri

Bayan da ya gama ziyarar aiki a kasar Rasha, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai fara ziyara a wasu kasashen dake tsakiyar nahiyar Asiya, inda zai halarci wasu muhimman taruka biyu, ciki har da taron kolin kungiyar hadin-kai ta Shanghai, gami da taron kolin kungiyar kara hadin-gwiwa da samun fahimtar juna ta kasashen Asiya. Sabbin manufofi da ra'ayoyin da shugaba Xi zai bayar a wajen tarukan biyu suna jan hankali sosai.

A shekara ta 2013, karon farko, shugaba Xi ya halarci taron kolin kungiyar hadin-kai ta Shanghai ko kuma SCO a takaice, inda ya bayyana wasu muhimman shawarwarin hadin-gwiwa da dama, ciki har da kafa bankin raya kungiyar SCO, da tattaunawa kan yarjejeniyar saukaka matakan kasuwanci da zuba jari. Ya ce kara samun fahimtar juna tsakanin kasashe membobin kungiyar SCO, da gudanar da hadin-gwiwa bisa adalci da mutunta juna, ya dace da zamanin da ake ciki da kuma moriya gami da bukatun jama'ar kasashen kungiyar.

Sai kuma a shekara ta 2014, lokacin da ake kara raya harkokin kungiyar SCO, shugaba Xi ya shawarci bangarori daban-daban su raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya, da kara kyautata tsarin kungiyar SCO, da kara budewa juna kofa. Shugaba Xi ya bada shawarar a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Asiya, da kokarin cimma burin neman bunkasuwa tare, da kara dankon zumunci tsakanin jama'ar kasashe daban-daban, gami da fadada hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin juna.

Yarda da juna, da kawowa juna moriya, da tabbatar da adalci, da yin shawarwari, gami da mutunta mabambantan al'adu, tare kuma da neman ci gaba tare, muhimman manufofi ne na ci gaban kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO. A yayin da yake halartar taron kolin kungiyar a shekara ta 2015, shugaba Xi ya bayyana cewa, wadannan manufofi sun kafa alkibla ga dangantakar kasa da kasa a wannan zamanin da muke ciki.

Xi ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su ci gaba da bin manufofin kungiyar SCO, da tabbatar da adalci da daidaito tsakaninsu, da kara budewa juna kofa, da mutunta hakkin juna, da dakatar da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, da warware sabani ta hanyar lumana, ta yadda za su samu bunkasuwa tare.

A wajen taron kolin kungiyar SCO wanda aka yi a shekara ta 2016, shugaba Xi ya ce, zurfafa hadin-gwiwa tsakanin kasashe membobin kungiyar na bukatar bin yayi, haka kuma ya ce, nahiyar Asiya na kara fuskantar wasu kalubaloli da dama, al'amarin dake bukatar hadin-gwiwar kasa da kasa. Xi ya ce ya kamata a kara fahimtar makomar kungiyar, da daidaita manfofin hadin-gwiwa a fannoni daban-daban.

A shekara ta 2017, kungiyar SCO ta kara karbar wasu kasashe biyu, ciki har da Indiya da Pakistan a matsayin membobinta. Haka kuma a wajen taron kolin kungiyar da aka yi a shekarar, Xi Jinping ya jaddada cewa, kamata ya yi kungiyar SCO ta kara bude kofa ga sauran kasashe da yankuna.

Shugaba Xi ya ce, Sin na goyon-bayan kungiyar SCO ta karfafa hadin-gwiwa tare da kasashe 'yan kallo da sauran wasu kasashe ta hanyoyi daban-daban, da amincewa da SCO ta ci gaba da habaka hadin-gwiwa da mu'amalarta da Majalisar Dinkin Duniya da sauran wasu kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, a wani kokari na tabbatar da dauwamammen ci gaba da zaman lafiya a duk fadin duniya baki daya.

A bara wato shekara ta 2018, an yi taron kolin kungiyar SCO a birnin Qingdao na kasar Sin, inda aka fitar da Sanarwar Qingdao, inda aka cimma ra'ayi iri daya na raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya, abun da ya zama babban burin da kasashe membobi 8 na kungiyar ke kokarin cimmawa. Shugaba Xi Jinping ya kuma bayyana wasu muhimman ra'ayoyi biyar na ci gaban kungiyar SCO, wadanda suka shafi neman bunkasuwa, da tabbatar da tsaro, da samun moriya tare, da raya al'adu, tare kuma da yadda ake tafiyar da harkokin duniya.

A ziyarar da shugaba Xi zai kai wasu kasashen dake tsakiyar Asiya a wannan karo, zai kuma halarci taron kolin kungiyar kara hadin-gwiwa da samun fahimtar juna ta kasashen Asiya ko kuma CICA a takaice, taron da zai maida hankali kan raya kyakkyawar makomar al'ummar kasashen Asiya ta bai daya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China