Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin Sin zai taimakawa dauwamammen ci gaban duniya
2019-06-08 20:13:04        cri

Jiya Jumma'a 7 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci cikakken taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya da aka gudana a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha, inda ya gabatar da wani jawabi mai taken "Nacewa ga burin samun dauwamammen ci gaba domin kafa duniya mai wadata".

A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya jaddada cewa, samun dauwamammen ci gaba dabara mafi dacewa da ake iya amfani da ita yayin da ake kokarin dakile matsalar da kasashen duniya ke fuskantar a halin da ake ciki yanzu, kasarsa tana son ci gaba da sanya kokari tare da sauran kasashen duniya domin gina tattalin arzikin duniya da zai dace da yanayin daukacin kasashen duniya, kana za ta kara mai da hankali kan moriyar al'ummomin kasashen duniya domin samar da alheri gare su, don haka ya dace a nacewa manufar raya tattalin arziki bisa tushen kiyaye muhalli, tare kuma da tabbatar da zaman lafiya dake tsakanin bil Adama da hallitu masu rai da marasa rai, yanzu haka kasar Sin ta gabatar da shirinta kan batun.

A watan Saumban shekarar 2015, MDD ta zartas da ajandar samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, inda aka tabbatar da burin raya duniya a fannoni 17, ciki har da karuwar tattalin arziki da raya zamantakewar al'umma da kuma kiyaye muhalli, lamarin da ya tsara taswirar samun dauwamammen ci gaba ga duniya. Yanzu haka yanayin duniya yana samun manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin shekaru dari daya da suka gabata, a karkashin irin wannan yanayi, ana kara mayar da hankali kan batun samun dauwamammen ci gaba a taron tattaunawar tattalin azikin duniya a Saint Petersburg, har shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi cikakken bayani kan manufar kasar Sin kan batun, manufar da za ta samar da dabara ga kasa da kasa domin su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, hakika duk wadannan sun nunawa al'ummomin kasashen duniya hikima da imani na shugaban wata babbar kasa.

Ra'ayin shugaba Xi Jinping na bude kofa ga kasashen waje a fannoni daban daban yana shafar batun bunkasa tattalin arziki. Wannan yana da muhimmanci bisa yanayin tsananta rikicin cinikayya, da batun kara bada kariya ga cinikayya. Shugaba Xi Jinping ya jaddada imanin Sin na kara bude kofa ga kasashen waje da sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya da kuma tabbatar da tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban. Kana ya bayyana cewa, Sin tana son more fasahohin nazarin kimiyya da fasaha ciki har fasahar 5G tare da kasa da kasa. Wannan ya shaida cewa, kasar Sin mai bin manufar bude kofa ce ga kasashen waje za ta sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki da kimiyya da fasaha na duniya.

Ra'ayin shugaba Xi Jinping na samun moriyar juna ba tare da nuna bambanci ba ga juna yana shafar batun bunkasuwar zamantakewar al'ummar kasa da kasa. Ko da yake ana samun ci gaba kan kayayyaki da fasahohi a duniya, amma akwai rashin daidaito a tsakanin wurare daban daban na kasa da kasa, da kuma tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu ci gaba. Idan aka aiwatar da ayyuka bisa tunanin maida kasa kanta a matsayin gaban kome, da yin watsi da sauran kasashe, sai dai za a rufe kofar saura da hanya kanta, hakan zai kawo illa ga makomar dan Adam.

A cikin jawabin, Xi ya tabbatar da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bada gudummawa a fannonin kawar da talauci, samar da guraben ayyukan yi, bada hidimomin sa kai, jin dadin jama'a, da ma kare halatattun hakkokin masara karfi, domin bada darasi ga ci gaban al'ummar sauran kasashen duniya, ta yadda za a amfanawa jama'arsu sosai.

Ra'ayin shugaba Xi na samun jituwa a tsakanin dan Adam da muhallin halittu ya shaida tunanin kasar Sin na kare muhalli, da ma kokarinta na warware matsalolin da suka shafi yanayi da muhalli. A cikin jawabinsa, Xi ya nanata ra'ayin "kiyaye muhalli shi ne raya tattalin arziki", da kokarin kasar Sin na neman samun iska da ruwa da ma kasa mai tsabta, da aiwatar da yarjejeniyar kudurin Paris da sauran ra'ayoyin bai daya da kasa da kasa suka cimma, lamarin da ya shaida aniya da imanin kasar Sin wajen cika alkawarinta da ma samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba.(Jamila Zainab Kande)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China