Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hulda tsakanin Sin da Rasha ta shiga sabon matsayin da zai kara tabbaci ga duniya
2019-06-07 16:33:33        cri

A ranar Laraba 5 ga watan nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, suka bayar da muhimmiyar sanarwa guda biyu cikin hadin gwiwa a birnin Moscow fadar mulkin Rasha, inda suka sanar da cewa, za su himmantu kan aikin raya huldar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare a sabon zamanin da ake ciki yanzu, domin kara karfafa yanayin tabbaci a fadin duniya.

Bana ake cika shekaru 70 tun bayan da kasashen Sin da Rasha suka daddale huldar diplomasiyya tsakaninsu, a cikin wadannan shekaru 70 da suka gabata, kasashen biyu suna fuskantar kalubale iri daban daban tare, haka kuma huldar amincin juna dake tsakaninsu ta samu ci gaba cikin lumana, har ta kasance abun koyi ga sauran kasashen duniya.

Shugabannin kasashen Sin da Rasha, sun taba jaddadawa sau da yawa cewa, a halin da ake ciki yanzu, huldar dake tsakanin sassan biyu ta shiga matsayin koli a tarihi.

Yanzu haka daukacin kasashen duniya suna fama da manyan sauye-sauyen da ba su taba ganin irinsu ba a cikin shekaru dari da suka gabata, a don haka ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Rasha, ya alamta cewa, sassan biyu suna kara mai da hankali kan huldar, wadda za ta kawo babban tasiri ga hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu, da kuma tsarin kasa da kasa baki daya.

Abu mafi muhimmanci yayin da ake raya huldar dake tsakanin Sin da Rasha a sabon zamanin da ake ciki, shi ne nuna aminci ga juna, tare kuma da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan da suka fi jawo hankalinsu duka, kana idan ana son cimma wannan buri, ya dace sassan biyu su kara karfafa hadin gwiwa, da cudanya dake tsakaninsu bisa shawarar ziri daya da hanya daya. Ban da haka, ya kamata sassan biyu su kara sauke nauyi bisa wuyansu, yayin da suke gudanar da harkokin kasashen duniya bisa tushen kiyaye tsarin kasa da kasa wanda ke karkashin jagorancin MDD, ta yadda za a kafa sabuwar huldar dake tsakanin kasa da kasa, da kuma al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil Adama. Duk wadannan ba ma kawai za su kara kyautata huldar dake tsakaninsu ba ne kawai, har ma za su taimake su wajen dakile matsala a fannin tsaro da kasashen biyu suke fuskantar.

Hakika bisa bunkasuwar huldar dake tsakanin Sin da Rasha, al'ummomin kasashen biyu za su ci babbar gajiya daga wannan fannin. Misali a shekarar bara da ta gabata, adadin cinikayyar dake tsakanin kasashen biyu ta kai dala biliyan 100, adadin da ya karu da kaso 27 cikin dari bisa na shekarar 2017. Kana an lura cewa, Sin da Rasha, suna taimakawa juna yayin da suke raya tattalin arzikin kasashen su, a don haka ya dace su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata.

A ranar 5 ga wata, lokacin da shugabannin kasashen biyu suka daddale muhimmiyar sanarwa, kasashensu su ma sun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu guda 23, wadanda ke shafar fannonin tattalin arziki da zuba jari da masana'antu, da ilmi da sauransu, ciki hadda aikin gina makamashin nukiliya cikin hadin gwiwa tsakanin Sin da Rasha, da kafa kamfanin samar da makamashi cikin hadin gwiwa wajen zuba jari a kasar Sin, da shigar da kasar Sin cikin aikin hakar iskar gas a yankin iyakokin duniya na arewa, da zuba jarin da yawansa zai kai dala biliyan 1, domin kafa asusun kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na Sin da Rasha da sauransu.

Mashawarcin shugaban Rasha kan tattalin arziki Sergey Glaziev yana ganin cewa, idan Sin da Rasha sun kara karfafa hadin gwiwar tattalin arzikin dake tsakaninsu, to adadin cinikayyar dake tsakaninsu a cikin shekaru biyar masu zuwa zai kai dala biliyan 200.

Haka zalika, ci gaban huldar dake tsakanin sassan biyu, zai sa kaimi kan hadin gwiwarsu a cikin harkokin duniya, hakika bisa matsayinsu na zaunannun mambobin kasashen kwamitin sulhun MDD, Sin da Rasaha suna nacewa kan matsayinsu kusan iri guda a kan harkokin kasa da kasa, a cikin shekaru 6 da suka gabata, shugabannnin kasashen Sin da Rasha sun taba yin ganawa da juna har sau sama da 20, haka kuma sun taba yin tattaunawa tsakaninsu kan muhimman harkokin duniya. Nan gaba kasashen biyu wato Sin da Rasha, za su yi kokari tare, domin kiyaye kwarjinin MDD, tare kuma da kara karfafa cudanyar dake tsakaninsu bisa tsarin kungiyar hadin gwiwar Shanghai, da kungiyar BRICS, da kuma rukunin G20, kana za su himmantu kan aikin raya shawarar ziri daya da hanya daya, da aikin raya kawancen tattalin arziki tsakanin kasashen Turai da Asiya, ta yadda za su samar da karin damammakin hadin gwiwa ga kasashen da abun ya shafa. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China