Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping da Putin sun halarci taron cika shekaru 70 da kulla huldar jakadanci tsakanin Sin da Rasha
2019-06-06 14:36:30        cri


Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sun halarci babban taron cika shekaru 70 da kulla dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashensu jiya Laraba a birnin Moscow, inda suka kalli wasannin kade-kade da raye-raye na murnar wannan rana.

Putin ya gabatar da jawabin dake cewa, a cikin shekaru 70 da kulla dangantakar jakadanci tsakanin Rasha da Sin, huldarsu na bunkasuwa yadda ya kamata. Kasashen biyu na nunawa juna goyon-baya da taimako, da ciyar da dangantakarsu gaba zuwa wani sabon matsayi wanda ba'a taba ganin irinsa ba a tarihi. Putin ya ce kasashen biyu sun daddale wata sanarwar hadin-gwiwa, da tsara babban buri na zurfafa hadin-gwiwa tsakaninsu. Rasha na son yin kokari tare da kasar Sin wajen kara samar da alfanu ga jama'arsu baki daya.

A nasa bangaren, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi mai taken "Yin kokari kafada da kafada, don bude sabon babi ga dangantakar kasashen Sin da Rasha a sabon zamani", inda ya ce:

"Yau, muna bikin murnar cika shekaru 70 da kulla dangantakar jakadanci tsakanin Sin da Rasha, rana ce dake da ma'anar tarihi ga dangantakar kasashen biyu. Ba zamu manta ba, a yayin yake-yaken kare kasar Rasha da kin harin Japan, sojoji gami da fararen hula na kasashen Sin da tsohuwar tarayyar Soviet sun fatattaki mahara cikin hadin-gwiwa, inda suka kulla dadadden zumunci mai zurfi tsakaninsu."

Xi ya kara da cewa, kashe garin ranar da aka kafa sabuwar kasar Sin wato Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, gwamnatin tsohuwar tarayyar Soviet ta amince gami da kulla huldar jakadanci da kasar Sin. Haka kuma yayin da Sin ke nuna himma da kwazo wajen gina kanta, akwai kwararru da masanan kasasr Rasha da dama wadanda suka taimakawa Sin wajen farfado da ayyukan masana'antu. Da aka shiga karni na 21, Sin da Rasha sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai muhimmancin gaske, wato yarjejeniyar hadin-gwiwa da sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Rasha, wadda ta ayyana ra'ayin "kulla zumunta zuriya bayan zuriya, kuma ba za su zama abokan gaba har abada ba" a matsayin doka.

Har wa yau, Xi Jinping da Putin sun sanar da bunkasa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni tsakanin Sin da Rasha a sabon zamanin da muke ciki, al'amarin da ya bude sabon babi ga ci gaban dangantakarsu. Xi Jinping ya nuna cewa:

"Yayin da ake kara raya dangantakar Sin da Rasha a sabon zamani da muke ciki, ya kamata a kara samun fahimtar juna, da kara nunawa juna goyon-baya a wasu batutuwan da suka shafi moriyarsu. Ya kamata a yi kokarin samun alfanu tare, da ci gaba da inganta alakar shawarar 'ziri daya da hanya daya' da kawancen kasashen Turai da Asiya ta fannin tattalin arziki. Ya zama a kara mu'amala tsakanin jama'ar Sin da Rasha, da kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya, domin raya duniya mai wadata da adalci, a wani kokari na kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa da raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya."

Bugu da kari, Xi Jinping ya jaddada cewa, tarihi na shekaru 70 ya shaida cewa, ko a da, ko a yanzu ko kuma a nan gaba, Sin da Rasha aminan arziki ne na ainihi. Ya kamata a himmatu kafada da kafada don samar da kyakkyawar makoma ta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni tsakanin Sin da Rasha a sabon zamanin da muke ciki.

Bayan da suka halarci babban taro na murnar cika shekaru 70 da kafa dangantakar jakadanci tsakanin kasashen Sin da Rasha, Xi da Putin sun kuma kalli wasannin kade-kade da raye-raye masu kayatarwa da masu fasahar kasashen biyu suka gabatar tare.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China