Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ci gaban da Sin take samu ta fuskar kyautata ingancin iska ya zama abin koyi ga sauran kasashe
2019-06-04 14:34:08        cri

A shekarun nan baya-baya, an cimma muradun kyautata ingancin iska a fannoni daban-daban bisa shirin yaki da gurbata iska a kasar Sin, matakin da ya gamsar da jama'a sosai, saboda ganin tsabtacciyar iskar da suke mora. To, wane irin ci gaba da kasar Sin take samu a wannan fanni? Kuma mene ne ra'ayoyin kasashen duniya kan wannan batu?

An ba da kididdiga cewa, muhimman abubuwa masu gurbata iska hudu ciki hadda ma'aunin gurbatar iska na PM2.5 sun ragu sosai a shekarar 2018, daga cikinsu matsakaicin ma'aunin PM2.5 ya kai 51μg ko wane cubic mita, inda sinadarin SO2 ya ragu zuwa wani sabon matsayi da ya kai 6μg a ko wane cubic mita. Mazauna birnin Beijing na farin ciki sosai da ganin irin wannan sauyi.

Tun daga shekarar 2013, Sin ta dauki matakai masu dimbin yawa a wannan fanni, ciki hadda kyautata tsare-tsare, sa kaimi ga yin kwaskwarima, kyautata dokoki, da kara sa ido. Ya zuwa karshen shekarar 2018, yawan ranekun da ake fama da tsananin gurbatacciyar iska ya ragu zuwa 15 daga 58, yayin da a birnin Tianjin, wannan adadi ya ragu zuwa 10 daga 49, a lardin Hebei kuma ya ragu daga 80 zuwa 17.

Shugaban sashe mai kula da harkokin iska na hukumar kiyaye muhalli na kasar Sin Liu Bingjiang ya ce, matsakaicin yawan ranekun da suka samu iska mai kyau na yawancin biranen Sin a bara ya kai kaso 80 cikin dari. Ya ce:

"An kyautata ingancin iska sosai bayan kokarin da dukkanin al'umma suka yi. A shekarar bara, matsakaicin ma'aunin PM2.5 na yawancin biranen Sin ya kai 39μg ko wane cubic mita, wanda ya ragu da kashi 9.3 cikin dari bisa na makamancin lokacin na shekarar 2017. A wasu yankunan dake kewayen birnin Beijing, Tianjin da lardin Hebei, da kuma yankin delta na kogin Yangtse da yankin filin Fenwei kuwa, wannan ma'aunin ya ragu da kashi 11.8 cikin dari, da kashi 10.2 cikin dari da kuma 10.8 cikin dari. A cikin birnin Beijing kuma, wannan adadi ya kai 51μg ko wane cubic mita wanda ya ragu da kashi 12.1 cikin dari bisa na makamancin lokacin na shekarar 2017. Ban da wannan kuma, matsakaicin raneku na samun iska mai inganci na birane 338 ya kai kashi 79.3 cikin dari, wanda ya fi yadda aka yi hasashe."

Shirin kiyaye ingancin iska na tsawon shekaru 3, shiri ne na kiyaye muhalli da gwamnatin Sin ta gabatar, da zummar kyautata ingancin iska cikin dogon lokaci. Ya zuwa yanzu, larduna 31 sun fitar da manufofin kiyaye muhalli, da kuma tabbatar da sauke nauyin kiyaye muhalli. A bana kuma, Sin ta ci gaba da yaki da gurbata iska da tabbatar da ci gaban da aka samu a wannan fanni, yawan gurbatacciyar iska da za a fitar zai ragu da kashi 3 bisa dari, yayin da kuma PM2.5 a wasu muhimman yankuna na ci gaba da raguwa. Ministan kiyaye muhallin halittu Li Ganjie ya ce:

"Ya kamata mu kara kwarin gwiwarmu da daukar karin matakai masu inganci don yaki da gurbatar muhalli cikin dogon lokaci, da kuma raya tattalin arziki mai inganci tare da kiyaye muhalli. Kana a kyautata muhalli don biyan bukatun jama'a na more rayuwa."

A matsayin kasa ta farko a duniya da ta dauki matakin yaki da PM2.5, Sin ta kafa mataki irin nata bisa fasahohin kasa da kasa da kuma hakikanin halin da take ciki, wato jama'a da kamfanoni da hukumomi daban-daban su sauke nauyin dake wuyansu karkashin jagorancin gwamnati. Mukadashin direkta mai kula da ayyukan tsai da shiri kan kiyaye muhalli na MDD Madam Joyce Msuya ta taba zama da aiki a kasar Sin har tsawon shekaru 4, tana gannin yadda kasar Sin ke gudanar da wannan aiki, a ganinta, fasahohin kasar Sin a fannin kyautata muhalli abin koyi ne ga sauran kasashe, ta ce:

"Sauran kasashe masu tasowa na kokarin fidda abubuwan da za su koya daga kasar Sin. Kiyaye ingancin iska bangare daya ne daga cikinsu, sauran fasahohi sun hada da yin amfani da albarkatun ruwa da makamashi, da kara dasa itatuwa a gadun daji da birane da kuma kafa lambunan shan iska da dai sauransu. Muna fatan ganin ci gaban da Sin za ta samu karkashin shirinta na 13 na kiyaye muhalli a cikin shekaru 5. "

Duniya daya tilo Bil Adam ke da ita, wayewar kan jama'a na bunkasuwa tare da muhalli. Sin kuma na shirin gudanar da shiri na 14 na ci gaban tattalin arziki da zaman al'ummar kasar cikin shekaru 5 wato daga shekarar 2021 zuwa 2025, ministan kiyaye muhallin halittu Li Ganjie na ganin cewa, wannan shiri na kasancewa matakin farko na kafa al'umma cikin wadata da kafa kasa ta zamani a dukkanin fannoni bayan Sin ta cimma muradun karni, kuma ya kasancewa a muhimmin lokaci da ake samun ci gaba wajen yaki da gurbatar muhahli da ci gaba da kafa kyakkyawar kasa mai kiyaye muhalli. Shiri na 14 na ci gaban tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin cikin shekaru 5 masu zuwa zai mai da hankali sosai kan kiyaye muhalli, raya kimiyya da fasahohi da kirkire-kirkire, da dora muhimmanci sosai kan rayawa da kuma kiyaye muhalli a cikin shekaru 5 masu zuwa har ma a dogon lokaci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China