Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana Sin da Afirka na fatan a kara yin tattaunawa kan shawarar "ziri daya da hanya daya"
2019-05-31 12:03:12        cri

A jiya Alhamis, an yi taron tattaunawa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" tsakanin masanan kasar Sin da Afirka a birnin Addis Ababa, hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka, wato AU. Kusoshi da jami'ai na gwamnatoci da masana da kuma wakilan jagororin masana'antu daga kasashen Sin da Afirka ne suka halarci taron.

Babban jigon wannan taro shi ne "yin tattaunawa da shimfida da kuma more shawarar 'ziri daya da hanya daya' tare domin bunkasa kasar Sin da kasashen Afirka tare". A yayin taron, jakada Liu Yuxi, shugaban tawagar kasar Sin a hedkwatar AU ya bayyana wa mahalarta taron sakamakon da aka samu a yayin taron koli karo na biyu na dandalin tattaunawar shawarar "ziri daya da hanya daya". Jakada Liu ya bayyana cewa, kasashen Afirka 39 da kungiyar tarayyar Afirka AU sun sanya hannu kan takardun yin hadin gwiwa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da bangaren Sin. Sakamakon haka, kawo yanzu, an riga an kaddamar da wasu layukan dogo da hanyoyin mota da gadoji da filayen saukar jiragen sama da yankin bunkasa masana'antu a wasu kasashen Afirka. Al'ummar Afirka sun fara cin gajiyarsu. Mr. Liu Yuxi yana mai cewa, "Mahalarta taron na ganin cewa, yanzu kasashen Afirka sun shiga lokacin bunkasa da kuma inganta tattalin arzikinsu. Kasashen Afirka na bukatar yin hadin gwiwa da sauran kasashen da gamayyar kasa da kasa wajen samar da kayayyakin more rayuwar al'umma da horar da kwararru da shigar da jari da dai sauran fannoni. A wannan taro, mun cimma matsaya daya kan yadda za a yi hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a fannonin bunkasa masana'antu da aikin gona na zamani da samar da karin kayayyakin more rayuwar al'umma tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Ya kamata kasashe masu tasowa su kara yin hadin kai, ta yadda za su martaba ka'idojin bunkasa tattalin arziki a duniya bai daya kamar yadda sauran kasashen duniya suke bi, sannan kuma su nuna adawa da kawo cikas ga ra'ayin cinikayyar da ake yi cikin 'yanci."

Shugaban asusun Seyoum, kana tsohon ministan harkokin wajen kasar Habasha Mr. Seyoum Mesfin ya bayyana cewa, kasashen Afirka sun shiga halin fama da talauci sakamakon mulkin mallaka da aka yi a Afirka har na tsawon wasu karni. Kasashen Afirka sun dade suna daidaita harkokin siyasa da bunkasa tattalin arzikinsu bisa hulda na rashin zaman daidai wa daida kuma maras adalci. Sakamakon haka, kayayyakin more rayuwar al'umma da ake da su a kasashen Afirka sun koma baya, tattalin arzikinsu ba shi da karfi, an tsara manufar bunkasa Afirka ta dogon lokaci bisa taimakon wasu kasashen duniya. Wadannan su ne alamar Afirka. Amma yanzu, ana gyara salon hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka sakamakon ci gaba da bunkasuwar da kasar Sin ta samu. An kuma samu sabon tunani kan yadda kasashen Afirka za su iya samun ci gaba.

"Hanyar da kasar Sin take bi wajen yin hadin gwiwa da kasashen Afirka wadda ta kawo sabon karfin bunkasa Afirka ta sha bamban da irin ta kasashen yammacin duniya. A cikin dimbin shekarun da suka gabata, hanyar da kasar Sin take bi tana taimakawa kasashen Afirka wajen inganta kayayyakin more rayuwar al'umma wadanda suka lalace, har ma tana samar da sabon tsarin yanar gizo. Yanzu, jerin hanyoyin mota da layukan dogo da ake shimfidawa a kasahen Afirka za su iya hada kasashen Afirka gaba daya. Bisa makudan jarin da ake zubawa da kyakkyawan hasashe na yin mu'amala a tsakanin kasashen duniya gaba daya, tabbas shawarar 'ziri daya da hanya daya' za ta kawo wa kasashen Afirka moriya. Tattalin arzikin duk duniya ma zai kara taimakawa juna. Kasashen Afirka za su iya yin amfani da wannan shawara wajen samun bunkasuwa."

Madam Amani Abou-Zeid, jami'a mai kula da harkokin kayayyakin more rayuwar al'umma da makamashi a kungiyar AU ta nanata cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" muhimmin shiri ne dake kokarin kafa wata al'umma mai makoma ta daya ga dukkanin bil Adama. Kungiyar AU za ta ci gaba da goyon bayan shawarar "ziri daya da hanya daya". Madam Amani Abou-Zeid tana mai cewa, "Ba ma kawai 'ziri daya da hanya daya' tana kokarin a kara hada wurare daban daban ba, har ma tana goyon bayan yin mu'amala tsakanin mutane. Shawarar wata wani muhiimin dandali ne a gare mu, tana bayar da gudummawa sosai wajen samar da karin kayayyakin more rayuwar al'umma ga kasashe da kungiyoyi da abin ya shafa, har ma tana bayar da gudummawa ga ayyukan shimfida zaman lafiya a duniya baki daya. Kungiyar AU na goyon bayan wannan shawara wadda take kokarin bunkasa duk duniya bai daya." (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China