Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
"Ciwon fargaba" na lalata tushen huldar Sin da Amurka
2019-05-26 20:53:26        cri

Shugaban jami'ar Yale ta kasar Amurka, Mr. Peter Salovey a kwanakin baya ya rubuta wata wasika ga al'ummar kasa da kasa, inda ya bayyana damuwarsa game da huldar dake cigaba da yin tsami tsakanin Amurka da Sin a cikin makonnin baya bayan nan, tare da jaddada cewa, bude kofa ga juna shi ne kadai tushen samun nasarar fitattun jami'o'in kasar Amurka, wanda kuma ita ce alama ta jami'ar ta Yale.

Wannan wasikar da Mr. Peter Salovey ya bayar ta nuna yadda cudanyar al'umma ke fuskantar karin barazana daga wasu 'yan Amurka dake fama da "ciwon fargaba". Ta bangaren ilmin kiwon lafiya, ciwon fargaba na nufin wadanda ke cikin yanayin tunani na yiwuwar fuskantar hari ko illa daga wasu, ciwon dake jefa su cikin zaman zullumi na shirin tinkarar wani hari a kullum. A cikin shekarar da ta gabata, yadda wasu 'yan siyasa na Amurka ke furuci tare da daukar matakan da ba su dace ba tamkar suna fama da ciwon fargaba ne. Yadda suke daukar kasar Sin a matsayin abokiyar gaba da yadda suke ta kokari kafa shingayen ciniki, da kuma yadda suke zargin kasar Sin da sata tare da zargin Sinawa dake dalibta a kasar da kasancewa 'yan leken asiri, lamarin da ya wuce tunanin dan Adam.

Cudanyar al'umma shi ne tushen dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, don haka babban tushe na bunkasa huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka yadda ya kamata, shi ne kara yin mu'amala a tsakanin jama'ar kasashen biyu. A kowace rana, mutane sama da dubu 14 suna zirga-zirga ta hanyar jiragen sama a tsakanin kasashen biyu, a kowace shekara kuma yawan mutanen kasashen biyu da suke mu'amala da juna ya wuce miliyan 5.3, kana biranen da suka kulla huldar kawance a tsakanin kasashen biyu sun wuce 400, dukkansu sun shaida yadda kasashen Sin da Amurka ke kara cudanya da juna.

Amma wadancan 'yan siyasa da suka kamu da ciwon fargaba, suna mayar da irin cudanya da ake yi a tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata a matsayin ayyukan da ke janyo musu fargaba, suna tayar da jita-jita, da bata sunan dalibai da masanan kasar Sin, sun ce wai su ne 'yan leken asali, har ma suna tsoratar da jama'arsu da harzuka jama'ar kasashen Sin da Amurka don su nuna gaba da juna, hakan yana lalata tushen dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Daga hana wasu masanan kasar Sin shiga Amurka, zuwa bukatar da ake yi cikin daftarin dokokin tsaron kasa na Amurka game da tsaurara ka'idojin ba da biza ga dalibai da masanan kasar Sin, har zuwa kayyade kafa kwalejin Confucius sakamakon zargin da take yiwa kasar Sin na wai kawo tasiri ga kafofin watsa labaru, ana iya gano cewa, wadannan 'yan siyasar Amurka suna nufin kara rufe kofar yin mu'amala a tsakanin kasarsu da Sin.

Amma duk da haka, masu idon basira ba zasu yarda da wadannan kalamai ko abun da Amurka ta yi na rashin tunani ba. Alkaluman sun nuna cewa, a shekaru tara da suka wuce, kasar Sin ta fi sauran kasashe fitar da yawan dalibanta zuwa Amurka karatu, kuma daga shekara ta 2017 zuwa ta 2018, yawan gudummawar da daliban kasar Sin suka bayar ga tattalin arzikin Amurka ya kai dala biliyan 13.9. Tashar Intanet ta manufofin diflomasiyya ta Amurka ta wallafa wani bayanin da mataimakin shehun malami daga jami'ar Massachusetts ta Amurka Paul Musgrave ya rubuta, inda ya ce, kasar Sin babbar kasuwa ce dake fitar da dalibanta zuwa makarantun Amurka, sai dai yadda gwamnatin Amurka ta kawo cikas ga daliban kasar Sin wadanda ke son yin karatu a Amurka, zai haifar da babban hadari ga makarantun gami da tsarin bada ilimi na kasar.

A cikin wasikar da shugaban jami'ar Yale Peter Salovey ya rubuta, ya jaddada wani abu na daban, wato Yale na son daukar dalibai da masana wadanda ke da makoma mai haske don su shiga cikin jami'ar, ta yadda zata kyautata duniyarmu ta yanzu da samar da alfanu ga al'umma masu zuwa a nan gaba. Peter Salovey ya jaddada cewa, jami'arsa zata ci gaba da maraba da dalibai da masana daga kasa da kasa don su shiga jami'ar.(Lubabatu, Bilkisu, Murtala)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China