2019-05-26 17:13:00 cri |
Wani kwararre dan kasar Lebanon kan batutuwan kasar Sin Mahmoud Raya, ya ce, yayin da take mu'amala da sauran kasashe, Amurka ta kan dauki matakan sanya takunkumin tattalin arziki da kara buga haraji kan hajojin sauran kasashe, da nufin kawo cikas ga cigaban sauran kasashe. Tankiyar cinikayyar kasashen Sin da Amurka ta riga ta yi babbar illa ga masana'antun kasashen biyu da na sauran kasashe masu ci gaban masana'antu, haka kuma akwai yiwuwar samun raguwar bukatun man fetur a duniya, abun da zai kara haifar da abubuwan rashin sanin tabbas ga tsarin tattalin arzikin kasashen Larabawa.
A nasa bangaren, kwararre kan batun kasar Sin na kasar Masar, Samy El Kamhawy na ganin cewa, matakan da gwamnatin Amurka ta dauka na bada kariya ga harkokin kasuwanci da kara buga haraji kan hajojin sauran kasashe zai iya lahanta tattalin arzikin duniya.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China