Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan siyasa kamar John Bolton na sanya kasar Amurka ba ta iya daidaita harkokin diflomasiyya bisa ka'idojin da ake bi ba
2019-05-25 20:28:58        cri

A kwanakin baya, farfesa Tom Nichols na kwalejin koyon ilmin aikin sojan teku na kasar Amurka ya wallafa wani bayani a jaridar "Today's America", inda ya nazarci ayyukan diflomasiyya da gwamnatin kasar Amurka ta yi a 'yan kwanakin baya, ya kuma samu sakamakon cewa, yanzu gwamnatin kasar Amurka ba ta iya rike ragamar aiwatar da manufofin diflomasiyya kamar yadda ya kamata. Bugu da kari, a lokacin da gwamantin take daidaita harkokin diflomasiyya a 'yan kwanakin baya, a kullum, a kan ji John Bolton, mai ba da shawarar tsaro ga shugaban kasar yana tsoma baki cikin harkokin diflomasiyya.

A matsayin wakilin masu tsattsauran ra'ayi na Amurka, a lokacin da yake mukamin wakilin dindindin na kasar Amurka a MDD, John Bolton ya taba bayyana cewa, "Idan kasar Amurka na son MDD ta taka rawa, za ta sanya ta ta taka rawa kamar yadda take so. Kuma hakan ne abun da ya kamata MDD ta yi. Saboda a wajen Amurka, magana daya kadai ce ke da muhimmanci, ita ce yadda za ta kare moriyarta. Idan ba ka son maganar, sai dai ka yi hakuri, amma shi ne hakikanin gaskiya." Bayan ya hau kan mukamin mai ba da shawarar tsaron kasar Amurka, John Bolton wanda ba shi da kunya ya ci gaba da bayar da jawabai kamar yadda yake so. Ya taba shelanta cewa, wai "makamai masu linzami na kasar Sin za su kawo barazana ga kasar Rasha", amma bangaren Rasha ya mayar masa martani cewa, wadanda za su kawo wa moriyar kasar Rasha barazana su ne kasar Amurka da kungiyar Nato, ba kasar Sin ba.

Hakika dai, ban da John Bolton, akwai sauran masu ra'ayi rikau wadanda ke mulkin manufofin diflomasiyyar Amurka, kamar Mike Pompeo, da Peter Navarro. Suna yunkurin ganin Amurka ta ci gaba da yin babakere a duniya, don haka su kan musunta alkawuran da suka yi, su kan rura wuta, har ma su kan yi karya da kuma shafa wa wasu kashin kaji. Amma abin da ya wuce zatonsu shi ne yanzu haka, duniyar na fuskantar babbar sauyin ba a taba ganin irinsa ba a baya. Yunkurinsu zai ci tura, don ba zai hana tafiyar zamani ba.

Yanzu ana kalubalanta da kuma kyautata tsarin siyasar duniya, wanda aka kafa karkashin shugabancin Amurka bayan yakin duniya na biyu, yayin da aka canza tsarin tattalin arzikin duniya. Wadanda suka saba da yin babakere kan komai da komai suna cikin matukar damuwa da tsoro. A cikin tsawon lokaci da ya wuce, kasar ta Amurka ta sha janye jikinta daga kungiyoyin kasa da kasa da kuma yarjejeniyoyin kasa da kasa, a yunkurin kafa sabbin ka'idojin duniya, don kiyaye moriyarta. Sa'an nan ta sha cin zalin kawayenta, har ma ta tsoratar da su tare da yi musu sharri. Har ila yau tana matsa wa kasar Rasha lamba tare da tayar da yakin ciniki da kasar Sin. Ta sanya wa kamfanonin Sin takunkumi don hana ci gaban Sin ta fuskar kimiyya da fasaha.

Game da wasu matsalolin da kasar Amurka ke fuskanta wajen babban gibin dake kasancewa tsakanin masu arziki da masu fama da talauci, da rashin daidaito tsakanin masu kera kayayyaki da wadanda ba na kayayyaki ba, da kuma karuwar sabanin sakamakon bambancin launin fata da dai sauransu, masu mulki na Washington suna da nufin warware su bisa hujjar kare moriyar fararen hula don cimma burinsu a fannin siyasa, amma a karshe dai ba su cimma nasara ba, a maimakon haka, aka kara tsanantar matsalolin, har ma ake nuna kiyayya ga juna tsakanin rukunonin dake bisa matsayi daban daban, kana aka tayar da sabani daban daban, hakan ya sa masu mulkin suka shiga wani mawuyacin hali wajen gudanar da harkokin kasa.

Hakikanin yanayin da duniya ke ciki, shi ne zamanin mallakar duniya da Amurke ke yi na wucewa. Amma, John Bolton da sauran masu sha'awar yake-yake suna ta tsayawa kan amfani da tsoffin dabaru don tinkarar sabbin matsaloli, wannan ya nuna cewa, ba su gane yanayin ci gaba da duniya ke ciki ba, kuma ba su da imani kan irin canjawarta. Ko shakka babu, sakamakon tayar da tashin hankali da suka yi, harkokin diplomasiyyar da kasar Amurka ke yi za su kawo kasar hadaruruka. (Sanusi Chen, Tasallah Yuan, Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China