Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaridar This Day ta jinjina hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Nijeriya bisa shawarar "ziri daya da hanya daya"
2019-05-21 16:24:56        cri


A ranar 19 ga wata, jaridar This Day ta Nijeriya ta wallafa wani sharhi mai taken "Cimma daidaito a tsakanin Abuja da Beijing zai taimaka ga tabbatar da shawarar ziri daya da hanya daya" da Bola A.Akinterinwa, tsohon shugaban cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Nijeriya ya rubuta.

Sharhin da ya ruwaito ra'ayoyin mahalarta taron mai taken "cimma ra'ayi daya tsakanin Abuja da Beijing", ko kuma Abuja-Beijing Consensus a Turance, wanda shugaban kamfanin jaridar Leadership Sam Nda-Isaiah ya ba da shawarar shirya shi, ya jinjina damar da shawarar nan ta ziri daya da hanya daya ta samar ga ci gaban Nijeriya, ya kuma yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta daidaita manufofinta na diplomasiyya, tare da yin amfani da damar da shawarar ta samar don gaggauta bunkasuwar kasar.

Sharhin ya ce, a watan da ya gabata ne aka gudanar da taron dandalin hadin kan kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, kuma kasashen da suka hada da kasashen Afirka 37 suna duba bukatunsu na bunkasa manyan ababen more rayuwa da kuma jawo jarin waje, don haka, lokaci ya yi da kasashen Afirka za su shiga cikin tsarin raya shawarar ziri daya da hanya daya.

Sharhin ya kara da cewa, a yayin taron "cimma ra'ayi daya tsakanin Abuja da Beijing" , mahalarta taron sun gabatar da wasu kundi mai kunshe da bayanai guda 9, inda aka tattauna yadda Nijeriya za ta shiga aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya". A yayin taron, bi da bi shugaban kwamitin kula da huldar da ke tsakanin Nijeriya da Sin a majalisar wakilan kasar Yusuf Buba Yakub, da tsohon ministan harkokin waje na kasar Aminu Bashir Wali sun bayyana cewa, yadda kasar Sin ke hulda da sauran kasashe ba tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gidansu ba ya burge su, musamman ma kasashe masu tasowa. Ya ce, kasar Sin na kulla huldar hadin kai da abota da kasashen duniya bisa hadin gwiwar cimma moriyar juna da ta gudanar da kasashen ta fannonin raya manyan ababen more rayuwa da ayyukan gona da kuma kiwon lafiya. Shawarar "ziri daya da hanya daya" ta samar da damar samun karin ci gaban tattalin arzikin duniya, wadda kuma ta samar da wani sabon dandali na yin cinikayya da zuba jari a tsakanin kasa da kasa, har wa yau ta samar da wata sabuwar hanyar kyautata tattalin arzikin duniya. Yadda kasar Sin ke kara karfin zuba jari da gudanar da harkokin ciniki a kasashen Afirka, zai iya samar da babbar dama ga kasashen. Kasancewarta kasuwar da ta fi samun damar bunkasuwa, ya kamata Nijeriya ta yi amfani da damar da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta samar, kuma ta yi koyi da fasahohin da kasar Sin ta samu, ta yadda za ta fid da al'ummarta daga talauci da kuma karfafa imaninsu da kuma yadda suke alfahari da kasar. Sharhin ya kara da cewa, a kokarin da gwamnatocin kasashen biyu da ma al'ummarsu suka yi, hadin gwiwar kasashen biyu na da makoma mai kyau, kuma tabbas kokarin farfado da Nijeriya zai tabbata.

Sharhin ya kuma ruwaito jakadan kasar Sin a Nijeriya Mr.Zhou Pingjian yana cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta samu goyon bayan kasa da kasa, kuma kasar Sin na son inganta dangantaka da mu'amala da juna da kuma hadin gwiwar tsaro a tsakaninta da Nijeriya, ta yadda kasashen biyu da kuma al'ummominsu za su ci gajiyar shawarar "ziri daya da hanya daya".

Shugaban kamfanin jaridar Leadership ta Nijeriya, Mista Sam Nda-Isaiah, shi ne ya shirya wannan taro mai taken "cimma ra'ayi daya tsakanin Abuja da Beijing", ko kuma Abuja-Beijing Consensus a Turance, da zummar kafa wata gada da za ta zurfafa zumuncin Sin da Nijeriya ta hanyar amfani da kwararru masu zaman kansu, ta yadda za a inganta hadin kan kasashen biyu a fannin gudanar da harkokin kasashen biyu da masana'antu da tsaron kasa da ba da ilmi da dai sauransu.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China