Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An shirya taro kan hadin gwiwar Sin da Nijeriya a Abuja
2019-05-20 14:36:49        cri

Kwanan baya, an shirya wani taro mai taken "cimma ra'ayi daya tsakanin Abuja da Beijing", ko kuma Abuja-Beijing Consensus a Turance a Abuja, hedkwatar kasar Nijeriya, inda aka tattauna kan shawarar "Ziri daya da hanya daya". Taron dai ya samu halartar manyan shugabannin kasar Nijeriya da ma masana da kafofin yada labarai na kasar, baya ga wakilan kamfanonin Sin dake Abuja da dama. Ga cikakken rahoton da abokiyar aikinmu Amina Xu ta hada mana dangane da taron.

Shugaban kamfanin jaridar Leadership ta Nijeriya, Mista Sam Nda-Isaiah, shi ya shirya wannan taro mai taken "cimma ra'ayi daya tsakanin Abuja da Beijing", ko kuma Abuja-Beijing Consensus a Turance, da zummar kafa wata gada da za ta zurfafa zumuncin Sin da Nijeriya ta hanyar amfani da kwararru masu zaman kanta, ta yadda za a dukufa kan hadin kan kasashen biyu a fannin gudanar da harkokin kasashen biyu da masana'antu da tsaron kasa da ba da ilmi da dai sauransu. Jakadan Sin dake Nijeriya Mista Zhou Pingjian, da shugaban kwamiti mai kula da dangantakar Sin da Nijeriya na majalisar wakilan kasar Mista Yusuf Buba Yakub, da kungiyar 'yan kasuwa Sinawa dake Nijeriya, da wakilan kamfanonin kasar Sin da ke Nijeriya, na daga cikin wadanda suka halarci taron.

Sam Nda-Isaiah, shugaban wannan taro, na ganin cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta kasance wani tsari dake iya hada kan Sin da duniya gaba daya don samun moriya tare, ya ce:

"Sin kasa ce a duniya da ta fi yawan zuba jari kan gina manyan ababen more rayuwa a ketare, wannan taro dai na da burin sa kaimi ga hadin kan Sin da Nijeriya da samun moriya tare, bunkasuwar Sin tana kawo tasiri sosai ga duniya."

A nasa jawabin, Jakada Zhou, ya yi bayyani kan taron dandalin tattauna hadin kan kasa da kasa karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya" karo na biyu, inda ya ce:

"An shiga sabon mataki na hadin kan kasa da kasa karkashin shawarar 'Ziri daya da hanya daya', wanda ya kawo babban zarafi ga hadin kan kasashen biyu. Sin na fatan kara tuntubar juna da zurfafa cudanyar jama'ar kasashen biyu da ingizi hadin kan kasashen ta fannin tsaro don kawo moriya ga jama'arsu."

Shugaban kwamitin kula da dangantakar Sin da Nijeriya na majalisar wakilan Nijeriya Mista Yusuf Buba Yakub na ganin cewa, wannan shawara ta samar da damar samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya da sabon dandalin cinikayyar kasa da kasa da zuba jari, kuma ta samar da wata sabuwar hanya ta daidaita matsalolin tattalin arzikin duniya gaba daya. Ya ce,

"Sin ta hada kanta da Nijeriya a karkashin tsarin dandalin tattauna hadin kan Sin da Afrika. Kamata ya yi, bangarorin biyu su kai ga sabon matsayi a wannan fanni a karkashin wannan shawara na 'Ziri daya da hanya daya'. Sin da Nijeriya sun kulla yarjejeniya yayin taron dandalin tattauna hadin kan kasa da kasa karkashin wannan shawara da aka yi a watan Afrilun bana, ba shakka Nijeriya ta zama wurin dake da makoma mai haske da Sin za ta zuba jari."

Shugaban kungiyar Sinawa 'yan kasuwa dake Nijeriya, kuma babban manajan reshen kamfanin CGCOC a Nijeriya, Mista Ye Shuijin, ya gabatar da jawabi yayin taron da aka yi a wannan rana, inda yake ganin cewa, kasancewarta babbar kasa a nahiyar Afirka ta fuskokin tattalin arziki da yawan mutane, bunkasuwar Nijeriya da hadin kanta da kasar Sin na da ma'ana sosai wajen ingiza hadin gwiwar Sin da Afrika da ma raya shawarar gaba daya. Ya ce:

"Sin da Nijeriya na samun ci gaba mai armashi a fannin gudanar da shawarar 'Ziri daya da hanya daya'. Yayin taron dandalin tattauna hadin kan kasa da kasa karkashin wannan shawara karo na biyu da aka yi a watan Afrilun bana, an tabbatar da burin samun bunkasuwa mai inganci da kulla dangantakar dake raya duniya tare, da ci gaba da kyautata tsarin hadin kai, matakin da ya alamta cewa, wannan an shiga sabon mataki wajen aiwatar da shawarar, kuma ya samar da tafarkin samun bunkasuwa mai inganci tsakanin Sin da Nijeriya, har ma ya bukaci kamfanonin Sin dake Nijeriya su kara kokarinsu."

Mahalarta taron 'yan Nijeriya, sun yi kira ga gwamnatin kasar da ma bangarori daban daban na kasar, da su yi koyi da kyawawan fasahohin kasar Sin wajen farfado da kasa da fitar da jama'a daga talauci. Suna ganin cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya", na kasancewa wani dandali mai bude kofa da kawo moriyar juna, kuma ya kamata Nijeriya ta yi amfani da zarafin don gaggauta bunkasuwar kasar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China