in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin dangin gyada giram 20 a ko wace rana yana iya rage barazanar kamuwa da cututtuka da dama
2018-01-21 10:17:17 cri

Mene ne za mu iya ci a ko wace rana domin kiwon lafiyarmu?

Masana ilimin kimiyya suna ta gudanar da nazari domin tabbatar da amfanin wani nau'in abinci ga lafiyar mutane. A Kwanakin baya, sakamakon wani nazari ya shaida cewa, cin dangogin gyada giram 20 a ko wace rana yana iya rage barazanar kamuwa da cututtuka da dama, kamar ciwon zuciya da ciwon sankara.

Masu nazari daga kwalejin nazarin kimiyya da fasaha ta kasar Birtaniya da jami'ar kimiyyya da fasaha ta kasar Norway sun kaddamar da rahoton nazarinsu dake cewa, idan mutum ya ci dangin gyada giram 20 a ko wace rana, to zai rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya da kusan kashi 30 cikin dari, kana zai rage barazanar kamuwa da ciwon sankara da kashi 15 cikin dari. Ban da haka kuma, watakila cin dangin gyada yana da nasaba da raguwar barazanar kamuwa da ciwon kayayyakin jiki masu taimakawa numfashi da ciwon sukari.

Masu nazarin sun tantance rahotannin nazari guda 29 da aka riga aka kaddamar da su a duniya, wadanda suka shafi mutane fiye da dubu 819 da dangin gyada iri daban daban. Masu nazarin sun yi nuni da cewa, ko da yake akwai bambanci a tsakanin mutane, amma galibi dai, cin dangin gyada yana da alaka da raguwar barazanar kamuwa da wasu cututtuka.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, dangin gyada yana amfanawa lafiyar mutane, watakila saboda suna kunshe da dimbin sinadarai masu gina jiki, wadanda suke taimakawa wajen rage yawan sinadarin Cholesterol da ke cikin jikin mutum da kuma barazanar kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini.

Amma duk da haka, wannan nazari ya nuna mana cewa, cin dangin gyada da yawa ba shi da amfani ga lafiyar mutane. Babu wata shaida da ke nuna cewa, idan mutum ya ci dangin gyada da yawansa ya wuce giram 20 a ko wace rana, sai za a kara amfanawa lafiyarsa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China