in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kusanci da muhallin halittu yana taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da ciwon bakin ciki
2016-02-07 13:09:44 cri

Wani sabon nazari da aka yi a kasar Amurka, ya shaida cewa yawo cikin muhallin halittu, yana taimakawa sosai wajen kasancewa cikin koshin lafiya a fannin tunanin dam Adam, lamarin da yake ba da taimako wajen rage barazanar kamuwa da ciwon bakin ciki. Sakamakon nazarin ya lalubo bakin zare game da sassauta illar da ci gaban birane yake haddasawa ga tunanin dan Adam.

Nazarin ya bayyana sakamakon dake tattare da bunkasuwar birane, wanda ke sanya yawan mutanen da ke fama da ciwon bakin ciki, da sauran matsalolin tunani ya karu kwarai da gaske. Masu nazari daga jami'ar Stanford ta kasar Amurka sun kaddamar da rahotonsu cikin jaridar kwalejen nazarin kimiyyar kasar Amurka, inda a cewarsu, sun gudanar da wani nazari da zummar gano alakar da ke tsakanin kusanci da muhallin halittu da kuma barazanar gamuwa da matsalolin tunani.

Masu nazarin sun raba mutane masu koshin lafiya zuwa rukunoni guda 2, inda suka bar su suka yi yawo na tsawon awa daya da rabi, rukuni na A sun yi yawo a filin mai shuke-shuke, inda aka dasa bishiyoyi da dama, yayin da rukuni na B suka yi yawo a hanyoyin birane, inda ke da cunkoson motoci. Bayan hakan ne kuma, masu nazarin suka auna musu saurin bugun zuciya da yawan yin numfashi, tare da daukar hoton kwakwalwarsu. Daga karshe masu nazarin sun gano cewa, wani sashe na kwakwalwar mutanen da suka yi yawo cikin muhallin halittu bai yi aiki fiye da kima ba, yayin da wannan sashen da ke kwakwalwar mutanen da suka yi yawo a birane ya yi aiki kamar yadda ya yi a baya.

Ana ganin cewa, yadda wannan sashen da ke kwakwalwar dan Adam ya yi aiki da yawa fiye da kima, yana da nasaba da barazanar gamuwa da matsalolin tunani.

Sakamakon nazarin ya shaida mana cewa, hakika dai kusanci da muhallin halittu yana iya taimakawa wajen daidaita sosuwar rai. Watakila za a iya gaya mana dalilin da ya sa muhallin halittu ya kan farantawa mutane rai. Har wa yau masu nazarin sun yi nuni da cewa, yayin da ake kokarin raya birane, ya zama wabiji masu tsara fasalin biranen su fahimci alakar da ke tsakanin kusanci muhallin halittu da kuma kasancewa cikin koshin lafiya a tunani, don haka watakila kebe wasu wuraren halitta a birane, zai ba da taimako wajen kare mazauna biranen daga gamuwa da matsalolin tunani. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China