Gundumar Kuche ta jihar Xinjiang tana da kyau

cri 2011-09-20 17:42:03

A ranar 19 ga wata, mun isa gundumar Kuche, wato tsohuwar kasar Qiu Ci cikin shekaru aru aru da suka gabata. Da farko dai, mun kai ziyara wata makarantar sakandare ta gundumar, wato makarantar sakandare ta ( 4 ) ta gundumar Kuche. Kusan, a cikin wannan makaranta, mun ga kome da kome, kamar su babban ginin dake gudanar da harkokin karatu, dakunan kwanan dalibai, dakin cin abinci da filayen motsa jiki, dukkansu sabbi ne.

Shugaban makarantar ya bayyana cewa, yanzu akwai dalibai 1900 da kuma malamai fiye da 130 da suke koyarwa a wannan makaranta. Bisa shirin da aka tsara, a nan gaba, za a dauki dalibai da yawansu zai kai dubu 4 da za su yi karatu a wannan makaranta.

A cikin babban ginin dake gudanar da harkokin karatu, ban da dakunan karatu, akwai dakunan koyon ilmin kwamfuta, da na zane-zane da na gwaje-gwajen ilmin sinadari da dai sauransu.

Lokacin da muka isa filayen motsa jiki 2, mun ga wasu dalibai suna wasan kwallon kwando, wasu kuma suna guje-guje da tsalle-tsalle.

Bayan makarantar sakandare ta 4 ta Kuche, mun kuma kai ziyara fadar sarkin Kuche da babban masallacin Kuche. Gundumar Kuche, shiyya ce da yawancin jama'ar da suke zaune a wurin musulmai ne. Sabo da haka, a da, yankin Kuche,yana da sarkinsa. Har yanzu sarkin karshe wanda ya kai shekaru 85 da haihuwa a bana yana raye. Mun kai masa ziyarar nuna girmamawa.

Bayan da muka ziyarci gundumar Kuche, Mr. Aghaeze Sunday ma'aikacin jaridar This Day ta kasar Najeriya ya ce, ya zuwa yanzu na ziyarci wasu wurare na jihar Xinjiang. A ganina, dukkan wuraren jihar suna da kyau. Jama'a suna jin dadin zamansu kamar yadda ya kamata, sannan jami'an gwamnatocin matakai daban daban suna aiki kamar yadda ake fata. Abubuwan da suka burge ni su ne, da farko, kasar Sin na aiwatar da shirin taimakawa juna a tsakanin yankunan kasar, wato yankuna masu arziki sun taimaki yankunan da har yanzu ba su samu ci gaba ba domin neman ci gaba tare. Sannan, kafin in zo nan kasar Sin, na ji an ce, kasar Sin kasa ce dake karkashin mulkin 'yan sanda. Amma, ya zuwa yanzu na shafe kwanaki 7 a nan kasar Sin, kuma na ziyarci wasu wurare a jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta, ban da 'yan sanda masu kula da harkokin zirga-zirga, ban ga 'yan sanda masu dauke da makamai da suke titunan biranen jihar ba, kuma kome na gudana daidai kamar yadda jama'a suke fata. Kasar Sin kasa ce mai girma sosai, ba karamar kasa ba ce. Sabo da haka, Mr. Sunday ya ce yana girmama gwamnatin kasar Sin sosai.

Sannan, Mr. Philip Alaba ma'aikacin jaridar The Guardian ta kasar Najeriya ya ce, bayan da ya yi kwanaki 6 yana aiki a jihar Xinjiang, yana mamakin yadda jama'ar jihar suke zaune lami lafiya. Jihar Xinjiang jiha ce mai girma sosai, wurare daban daban na jihar suna da halayensu na musamman, kamar misali, tafkin Tianchi dake kusa da birnin Urumqi, yana saman dutsen Tianshan, tafkin na samun ruwa ne daga kankarar dake kan kolin dutsen. Sannan, a gundumar Weili, mun kai ziyara kauyen Lopnur dake cikin hamadan Tarim. Kogin Tarim ya ratsa wannan kauye. Ka ga jama'a da kogi da hamada da bishiyoyi suna kasancewa cikin daidaito.

Bugu da kari, mista Philip ya bayyana cewa, yanzu yana son jihar Xinjiang kwarai. A nan akwai zaman lafiya. Jama'a suna wasa a kan titi da dare ba tare da wata tsangwama ba, kuma jama'ar kabilu daban daban suna zaune tare da juna cikin lumana.

Sanusi Chen daga gundumar Kuche ta jihar Xinjiang ta kabilar Uyghur mai cin gashin kanta. (Sanusi Chen)

© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China