|
||
![]() |
Saboda irin kyawun yanayi da sirrai iri-iri da suka hadar da fulawoyi masu ban sha`awa da yankin keda su, ya sanya a ko wanne lokaci yake daukar hankulan baki `yan yawon bude idanu dake shigowa nan kasar Sin a kullum.
Akwai tsaunuka daban daban wadanda suke zubo da ruwa, wani lokaci ma irin wadannan tsaunuka a kan samu daskararrar kankara mai ban sha`awa a wasu bangarori na tsaunukan
Wani lokaci a kan hango launin shudi daga saman wadannan tsaunuka, dake dauke da tsirrai da itatuwa daban daban.
Kamar dai yadda yake kunshe cikin rahotannin da wasu daga cikin `yan jaridu masu daukar huto `yan Najeriya suka bayar, jim kadan da kammala ziyararsu a nan kasar Sin, sun danganta gabar teku na Xinjiang tamkar yankin shakatawa na Obudu dake jihar Calabar a tarayyar Najeriya.
Duk da cewa dai yankin na Xinjiang yana da arzikin kifi, a don haka sau da dama mazauna wannan yankin sun camfa yin su bayan faduwar rana.
Daga karshe tawagar `yan jaridu masu daukar hotu, sun kara tabbatar da cewa, gabar teku na Xingjiang, wuri ne daya kamata masu zuwa kasar Sin da nufin yawon bude idanu su ziyarta, kuma babu shakka yankin zai iya kasancewa daya daga cikin fitattun wuraren bude idanu na duniya.(Marubuci: Sunday Aghaeze Mai fassara Bagwai)