|
||
![]() |
A wani kauye mai suna Qiaka dake gundumar Hetian ta jihar Xinjiang, akwai wata cibiyar yin ado kan tufafi ta hanyar amfani da allura da zare. A cikin cibiyar, akwai wata 'yar kabilar Uyghur mai kula da ayyukan dinki, sunanta Tursun Nishakhan, mai shekaru 53 a duniya.
Yanzu mu ga menene Madam Tursun ta fada:
"Na fara dinka tufafi da kaina tun lokacin da nike da shekaru 12 da haihuwa. A wancan lokaci, na koyi fasahar dinki daga wani tsohon malami a birnin Hetian. A shekarar da ta gabata, an kafa wata cibiyar yin ado kan tufafi ta hanyar amfani da zare da allura a kauyenmu, kuma an ba mu horo da darussa a wannan fanni."
To, wadanne irin ayyuka ne mutane su kan yi a wannan cibiya? A nata bangaren, darektar ofishin kula da harkokin mata dake gundumar Hetian Madam Gehemanisha Sadik ta gayawa wakilinmu cewa:
"Yanzu akwai ma'aikata 140 wadanda suke aiki a wannan cibiya, kuma aikin da su kan yi a kowace rana shi ne samar da tufafin yara kanana da matasa. Yawan kudin da kowane ma'aikaci ya kan samu a kowace rana ya kai Yuan akalla 50, har ma wasu su kan samu Yuan sama da dari a kowace rana."