|
||
![]() |
Ibrahim: To, malam Sanusi. Jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur tana arewa maso yammacin kasar Sin ne , kuma ta yi iyaka da kasashe takwas, ciki har da Rasha da Kazakhstan da Kyrghizstan da Tajikistan da Pakistan da Mangoliya da Indiya da kuma Afghanistan.
Haka kuma, Fadin jihar Xinjiang ya kai murabba'in kilomita miliyan 1 da dubu 660, wanda ya kai kashi daya daga cikin kashi shida na fadin kasar Sin baki daya, abin da ya sanya jihar a matsayin jiha mafi fadi a kasar Sin.
Sanusi: e, malam Ibrahim. Bugu da kari, Allah ya albarkaci jihar Xinjiang da albarkatun kasa kamar Tagulla da Dalma da Kwano da Kwal da Azurfa da Zinare da sauransu baya ga koramu da tabkuna da sauran halittu. Har ila yankin Xinjiang ya yi suna wajen samar da 'ya'yan itatuwa kamar Lemo da Inabi da Tufa baya ga Alkama da kuma Auduga da ake nomawa a yankin.
Ibrahim: Sannan, wani batu malam Sanusi shi ne, yawan mutanen dake jihar ya kai kimanin miliyan 20 da dubu 951, kuma daga cikinsu, kashi 60.7 cikin 100 sun kasance 'yan kananan kabilu ne. Tun zamanin da, Xinjiang wuri ne da kabilu da dama ke zaman cude-ni-in-cude-ka, kuma a halin yanzu Xinjiang tana da kabilun da yawansu ya kai 47, musamman ma kabilu 13 wadanda suka fara zama a jihar tun kaka da kakanni, ciki har da Uygur da Han da Kazak da Hui da Khalkhas da Mongoliya da Tajik da Xibe da Man da Uzbek da Rasha da kuma Tartar.
Sanusi:Malam Ibrahim, Na ji an ce, jihar Xinjiang jiha ce mai arzikin wuraren yawon shakatawa, ko za ka iya bayyana mana yaya ake raya harkokin yawon shakatawa a jihar?
Ibrahim: To, alkaluma sun nuna cewa, a farkon rabin shekarar 2010 yawan masu yawon shakatawa daga gida da ketare da suka ziyarci jihar ya kai miliyan 10, wannan ya karu da kashi 9 cikin 100 bisa na shekarar 2009, kuma yawan kudin da aka samu daga yawon shakatawa ya kai kudin Sin Yuan biliyan 10.2, wannan adadi ya karu da kashi 10 cikin 100 bisa na shekarar 2009. Wani muhimmin abu da ya kasance a jihar ta Xinjiang shi ne na tsauni mafi girma na biyu a duniya mai tsayin mita dubu 8 da 511 dake kudu da Xinjiang a iyaka da kasar Pakistan. Sannan akwai tsoffin wuraren tarihi da yawansu ya kai kimanin 236.