in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barkewar Batun 9•18 a ranar 18 ga watan Satumba na shekarar 1931
2015-08-31 15:54:51 cri

A ranar 18 ga watan Satumban shekarar 1931, da gangan ne sojojin kasar Japan suka lalata wani layin dogo dake yankin Liutiaohu na birnin Shenyang dake arewa maso gabashin kasar Sin, inda suka kaddamar da Batun 9•18, wanda ya kasance muhimmiyar alamar kai hari ga kasar Sin. Harin kuma da ya samu babbar tirjiya daga jama'ar kasar Sin, wadanda tun daga lokacin suka kwashe shekaru 14 suna kokarin kin amincewa da harin sojojin Japan. Sabo da haka, batun 9.18 ya kasance masomin yakin kin jinin harin sojojin Japan da jama'ar kasar Sin suka yi, wanda kuma ya nuna asilin barkewar yakin Fascist na duniya.

Mamaye yankin arewa maso gabashin kasar Sin, wani muhimmin mataki ne cikin manufofin kasar Japan na neman mallakar nahiyar Asiya, har ma duk duniya baki daya. Bayan gudanar da wasu shirye-shiryensu, karfe 10 da minti 20 na daren ranar 18 ga watan Satumba na shekarar 1931, sojojin Japan sun yi amfani da kananan nakiyoyi masu launin rawaye 42 wajen lalata layin dogo na Nan Man da ya rasta ta yankin Liutiaohu.

Yankin Liutiaohu yana da nisan kilomita 2.5 daga arewa da birnin Shenyang da ke kasar Sin, kuma yana kusa da sansanin Beida na rundunar sojin kasar Sin da aka girke su a yankin arewa maso gabashin kasar. Sabo da haka, sojojin kasar Japan sun zargi wadannan sojoji, tare kuma da jefa musu boma bomai, kana sun ba da umurni ga wani ayarin sojojin kasar da ke kusa da yankin Liutiaohu da ya kai farmaki kan ayarin sojojin kasar Sin da ke sashen arewa maso gabashin kasar.

Da misali karfe 11 na dare, mataimakin kwamanda dake kula da yankin Fengtian na kasar Japan karamin kanar Tadashi Hanaya ya saci sunan babban janar Kenji Dolhara wanda yake birnin Tokyo, ya aika da sakwanni ga babban hafsan-hafsoshin yankin Kwantung, da shugaban sojojin kasarsu cikin gaggawa, inda ya yi karyar cewa, a daren ranar 18 ga wata da misali karfe 10 da rabi, a yankin dake yamma da sansanin Beida da ke yankin Fengtian, sojojin kasar Sin sun bata hanyoyin jiragen kasa da Japan ta gina, inda suka kai farmaki ga sojojin Japan, kuma suka yi artabu da sojojin kasar.

Hedkwatar rundunar sojan Kwantung ta kasar Japan ta ba da umurni ga rundunarta masu jiran ko ta kwana mai zaman kanta rukuni na 2 da ta 5, da kuma kungiyar hadin gwiwa ta 29 ta bangare sojan kasar na biyu da su kai hare-hare a sansanin soja dake Beida, da kuma birnin Shenyang. Sa'an nan kuma, da karfe uku da rabi na safiyar ranar 19, kwanandan hedkwatar rundunar sojan Kwantung dake birnin Lvshun na kasar Sin Honjo Shigeru, ya isa lardin Shenyang domin ba da jagoranci kan yakin.

Haka kuma, bisa goyon bayan da sauran rundunonin sojojin kasar Japan suka ba ta, rundunar soji ta masu jiran kota kwana mai zaman kanta rukuni na daya, ta ci gaba da kai hari a sansanin soja dake Beida na kasar Sin. Daga bisani kuma, a ranar 19 da safe, sojojin Japan sun mamaye sansanin sojan Beida gaba daya.

A lokacin, ko da yake ana fuskantar yanayi mai tsanani a kasar Sin, sabanin rikici dake tsakanin kasar Sin da Japan ya ci gaba da karuwa, amma jam'iyyar Kuomintang ta Sin dake karkashin jagorancin Jiang Jieshi ta tsaya tsayin daka kan manufa ta "dacewar warware matsalolin cikin gida da farko, kafin a shiga yaki da sojojin ketare", lamarin da ya sa, jam'iyyar ba ta dauki mataki ko kadan ba domin tinkarar hare-haren da sojojin Japan suka kaiwa Sin.

Shi ya sa lokacin da sojojin Japan suka yi wa sansanin Beida kawanya, mafi yawan sojojin tawaga 7 ta yankin arewa maso gabashin kasar Sin sama da su dubu 7 ba su yi gwagwarmaya ko kadan ba, sabo da umurnin da aka bayar, amma wasu sun mai da martani, inda aka kashe tare da raunata sojojin Japan 24 baki daya. Wannan ya zama abin da ya haddasa matsalar "9•18".

A ranar 19 ga watan Satumba da misalin karfe 12 da minti 50 na tsakiyar dare, an kebe rundunar sojan Japan zuwa rundunoni uku domin kai hari kan birnin Shenyang. Sojojin rundunar soja na yankin arewa maso gabashin kasar Sin, da 'yan sanda da sauransu sama da dubu 9 dake ba da kariya ga birnin Shenyang, ba su yi gwagwarmaya da sojojin Japan ba, bisa umurnin rundunar da mahukuntan jam'iyyar Kuomintang suka bayar. Ya zuwa karfe 6 da minti 30 na safe na wannan rana, sojojin Japan sun shafe awoyi 5 kafin su kai ga mamaye birnin Shenyang. Daga bisani, bayan watanni 4 da kwanaki 18, suka samu mamaye duk yankin arewa maso gabashin kasar Sin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China