in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarkin kasar Japan ya sanar da mika wuya ba tare da wani sharadi ba
2015-08-26 15:07:04 cri

A ranar 15 ga watan Agustar shekarar 1945, sarkin kasar Japan ya sanar da mika wuya ba tare da wani sharadi ba.

A watan Agusta na shekarar 1945, a sakamakon yadda sojojin kasar Sin suka fara daukar matakan kin harin sojojin kasar Japan daga dukan fannoni, kasar Rasha kuma ta shiga yakin kin jinin Japan, kana kasar Amurka ta harba boma-boman nukiliya guda biyu a biranen Hiroshima da Nagasaki, ya sa kasar Japan ta amince da sanarwar Potsdam, wadda gwamnatocin kasashen Sin da Amurka da Ingila da kuma Rasha suka kulla.

A ranar 9 ga watan Agusta da karfe 10 da rabi, kasar Japan ta kira taron koli na jagorancin yaki, domin tattauna batun ci gaba da yaki ko mika wuya. Inda bangaren soja, da ma'aikatar harkokin waje na kasar Japan suka samu bambanci ra'ayi kan wannan batu, ya zuwa karfe 3 na ranar 10 ga wata, sarkin kasar ya yanke shawarar amincewa da sanarwar Potsdam, da sharadin zai iya ci gaba da sarrafa mulkin kasar Japan.

A ranar 10 ga watan Agusta da karfe 7 da kwata na safe, ma'aikatar harkokin wajen kasar Japan ta fidda sanarwar cewar Japan ta amince da sanarwar Potsdam, tare da umartar babban jami'in diplomasiyya na kasar dake kasar Switzerland Toshikazu Kase, da babban jami'in diplomasiyya na kasar dake kasar Sweden Okamoto, da su isar da sanarwar ga kasashen Sin, Amurka, Ingila da Soviet Union.

A ranar 12 ga watan Agusta da karfe 1 sauran minti 15 na tsakan dare, manyan jami'an soja na kasar Japan sun saurari amsar da kasashen hudu suka gabatar ga Japan, game da sanarwar ta hanyar rediyon kasar Amurka. A ranar 14 ga watan Agusta da karfe 11 sauran minti 10 na safe, kasar Japan ta kira taro na karshe a gaban sarkin kasar, sarkin kasar ya san yanayin da ake ciki, don haka ya amince da amsar da kasashen hudu suka gabatar ga Japan, kuma ya bada umurni ga gwamnatin kasar da ta tsara takardar tsagaita bude wuta.

Lokacin da gwamnatin kasar Japan ta yi shirin mika wuya, masu tsattsauran ra'ayi da masu taurin kai na fascist, sun yi yunkurin aiwatar da wata makarkashiya ta juyin mulki domin hana gwamnatin mika wuya.

Daga daren ranar 14 ga wata zuwa safiyar 15 ga wata, sojoji matasa sun yi juyin mulki, har ma suka harbi shugaban rundunar soja saboda ya ba da umurni da sunansa, a kewaye fadar sarki, da kwace faifan CD dake dauke da muryar sarkin kasar Japan ya na ba da umurnin mika wuya, tare da yin yunkurin kai hari kan masu ra'ayin wanzar da zaman lafiya a kasar, amma shan kayen da Japan ta yi abu ne da ba za a iya canjawa ba, kuma mataki ne da bai sami izni daga shugabannin sojojin, wadanda kuma suka ba da umurnin dakile su ba.

Korechika Anami, janar mai kula da rundunar sojojin kasar Japan wanda ke da hannu cikin wannan lamari ya kashe kansa a safiyar ranar 15 ga watan Agusta. Kuma a tsakiyar ranar 15 ga watan Agusta, aka watsa muryar sarkin Japan Hirohito da aka dauka ga dukkanin jama'ar kasar Japan, hakan ya nuna Japan ta mika wuya ba tare da ko wane irin sharadi ba.

A ranar 15 ga watan Agusta, majalisar ministocin Suzuki ta yi murabus. Daga baya kuma a ranar 17 ga wata, aka kafa sabuwar majalisar ministoci dake karkashin shugabancin babban janar na sojojin kasa Naruhiko Higashikuni, kana Shigemitsu Mamoru ya dare kujerar ministan harkokin waje. A wannan rana kuma, sarkin kasar Japan ya bayar da umurni ga dukkan sojojin ruwa da na kasa, da su mika wuya bisa sanarwar kawo karshen yaki.

Ya zuwa tsakiyar watan Satumba, sojojin kasar Japan sama da miliyan 3 dake yankin gabas mai nisa, da kasashen dake kudu maso gabashin Asiya, da yankin kudancin Pacific, da tsibiran dake Pacific sun mika wuya daya bayan daya ga kasashen kawancen.

Wannan labari na mika wuya da Japan ta yi ya samu yaduwa a dukkan kasar Sin, Sinawa da suka tsaya tsayin daka cikin yakin tsahon lokaci, da kuma wadanda suka sha wahala sakamakon yakin sun yi farin ciki sosai, sun kuma nuna murna matuka ta hanyoyi daban daban bisa wannan babbar nasarar yaki ta kin harin Japan. (Bilkisu, Lami, Zainab, Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China