in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin Lugouqiao: Mafarin kin jinin harin sojojin Japan da Sinawa suka kaddamar
2015-08-25 12:12:05 cri

A ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1937 ne sojojin kasar Sin suka nuna turjiya sosai ga harin da sojojin Japan suka kaddamar a Lugouqiao, lamarin da ya kasance mafarin yakin nuna kin jinin harin sojojin Japan.

Lugouqiao ko gadar Marco Polo kamar yadda ake kira, yana kudu maso yammacin birnin Beijing wadda a baya ake da suna Peking. Kafin aukuwar wannan lamari, Japan ta girke sojojinta a Rehe da kuma yankin gabashin lardin Chahar daga yamma. A daya hannun kuma, dakarun kasar Japan 40,000 na rike da arewa maso yammaci. Kana wasu dakarun kasar ta Japan 5,000 sun taru a tsakanin hanyar jirgin kasan da ta taso daga Peking zuwa Shanhaiguan.

A bangaren kasar Sin kuma, bataliya ta 29 ta girke dakaru 10,000 a lardunan Hebei da Chahar da kuma biranen Peking da Tianjin.

A kokarin da take yi na maimaita abin da ya faru a ranar 18 ga watan Satumban shekarar 1931, sojojin Japan sun kaddamar da hare-hare da dama a wajen arewacin garin Wanping da nufin kwace gari na Wanping. Ko da yake sojojin kasar Sin sun kimtsawa shirin yakin sojojin na Japan.

Da jijjifin ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1937, wani rukunin sojojin Japan masu sarrafa tankokin yaki sun tunkari bataliyar sojojin Sin da ke kusa da Lugouqiao, inda suka kai musu farmaki. Da misalin karfe 10 da minti 40 na yammacin wannan rana ne sojojin kasar Japan suka yi karyar cewa, wai daya daga cikin sojojinsu ya bata a lokacin wannan bata kashi, don haka suna bukatar iznin shiga garin Wanping domin su gudanar da bincike. Ko da yake bataliya ta 219 ta birget ta 110 da ke karkashin runduna ta 37 ta sojojin kasar Sin sun ki amincewa da wannan bukata ta sojojin Japan.

Da tsakar daren wannan rana, sai wani jami'in kasar Japan da ke Peking ya kira mahukuntan lardunan Hebei da Chahar na kasar Sin, inda ya bukace su da su ba su iznin shiga garin Wanping don gudanar da bincike kan sojan da suke ikirarin bacewarsa ba tare da bata lokaci ba. Sai dai Sinawan sun yi watsi da wannan bukata. Bayan wani dan lokaci sai jami'in na Japan ya sake buga waya ga hukumomin na Sin, inda ya yi barazanar cewa, muddin ba a bar su izinin shiga garin Wanping ba, to ba makawa sojojin Japan za su shiga garin da karfin tsiya su kuma gudanar da bincike a cikin garin.

Domin gudun abin da zai biyo baya, sai bangaren Sin ya cimma daidaito da bangaren Japan inda suka amince a gudanar da bincike kan lamari. A yayin da ake ci gaba da wannan batu, sai bangaren Japan ya samu labarin cewa, sojan da yake ikirarin cewa ya bata yanzu ya dawo. Amma duk da haka, ba su daddara ba, inda suka bukaci sojojin kasar Sin da aka girke a mashigar garin Wanping daga yamma da su janye, amma sojojin sun ki amincewa da wannan bukata.

Da misali karfe 5 na asubahin ranar 8 ga watan Yuli, kwatsam sai sojojin Japan suka yi luguden wuta kan garin Wanping, lamarin da ya tilastawa sojojin kasar Sin mayar da martani da nufin kare kansu kan harin na sojojin Japan, wannan shi ne ya haifar da barkewar yakin nuna adawa da mamayar da sojojin Japan suka yi kan Sinawa.

Shaidu na cewa, da gangan sojojin Japan suka kaddamar da harin Lugouqiao saboda manufofin Japan na mamaye yankuna ko kasashe, mai taken "manufofin nahiyoyi". Burin masu ra'ayin fascists na Japan a ko da yau she shi ne su yaki kasar Sin kana muhimmin yunkuri ko mataki na yakar duniya.

A wancan lokaci kasashen Jamus da Japan da masu ra'ayin nuna karfin tuwo na kasar Italiya sun kafa wani kawance, inda rikicin ya koma tsakanin dakaru masu ra'ayin nuna karfin tuwo ko Fascists da ragowar kasashen duniya.

A wannan yanayi da ake ciki, yadda Japan ta mamaye kasar Sin ba wai fada ne tsakanin kasashen biyu ba, amma shi ne mafarin yakin duniya na biyu. Kuma a daidai lokacin da wani bangaren kasar Sin ke fuskantar barazana, nan da nan jam'iyyar Koumintang da JKS suka hanzarta yiwa manufofinsu na jam'iyya gyaran fuska tare da fara shimfida turbar yin hadin gwiwa. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China