in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta shiga taron tsara kundin tsarin mulkin MDD
2015-08-13 16:33:21 cri

A ranar 25 ga watan Afrilu na shekarar 1945 ne kasar Sin da kasashen Amurka, da Birtaniya da tsohuwar tarayyar Soviet, suka shirya taron San Francisco, taron da wakilai daga kasashe 50 suka halarta, domin tattaunawa game da tsara kundin tsarin mulkin MDD.

A wancan lokaci kasar Sin ta aike da tawaga karkashin shugabancin Song Ziwen domin halartar taron. A matsayin wakilin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma mamban tawagar, Dong Biwu shi ma ya halarci taron.

A ranar 30 ga watan Oktobar shekarar 1943 kuwa, kasashen Sin, da tsohuwar tarayyar Soviet, da Amurka, da Birtaniya, sun daddale wata sanarwar tsaro a birnin Moscow, inda aka bayyana cewa, kasashen 4 za su kafa wata kungiyar kasa da kasa, don tabbatar da zaman lafiya da lumana a lokacin da ya dace. An kuma amince da shigar manya da kananan kasashen duniya cikin aiwatar da sha'awar zaman lafiyan.

Wannan shi ne karo na biyu, da Sin ta shiga ayyukan daddale yarjejeniyoyin kasa da kasa a matsayin wata muhimmiyar kasa, bayan da aka daddale yarjejeniyar hadin gwiwar kasashen duniya a watan Janairun shekarar 1942.

Daga watan Agusta zuwa na Oktobar shekarar 1944, wakilan kasashen Sin, Amurka, Birtaniya, da tsohuwar tarayyar Soviet sun gudanar da wani taro a Dumbarton Oaks dake dab da birnin Washington na kasar Amurka, inda suka tsara daftarin kundin da za a bi, wajen kafa hukumomin majalisar dinkin duniya.

Bayan taron, kasashen 4 sun sanar da kundin "shawarwari ga kafuwar wata babbar kungiyar kasa da kasa", wanda ya tabbatar da sunan wannan sabuwar kungiya, wato "majalisar dinkin duniya", tare da kebe wata kujera ta din din din a kwamitin sulhu na majalisar domin kasar Sin.

A ranar 25 ga watan Afrilun shekarar 1945, an kira taron kafa kundin tsarin aikin MDD a birnin San Francisco na kasar Amurka. A yayin wannan taro ne kuma tawagar kasar Sin mai kunshe da manyan kusoshin kasar 10, wadanda suka hada da Tse-ven Soong, da Vi Kyuin "Wellington" Koo, da Wang Chonghui, da Wei Daoming, da Dong Biwu, da Hu Shih, da dai sauransu, suka tsaya kan manufofin adalci da gaskiya, inda suka taimaka wajen cimma nasarar taron.

Ga misali, yayin da ake tattauna batun sanya wasu yankuna karkarshin kulawar wasu kasashe daban daban, wakilan kasar Sin sun bayyana cewa, kamata a sanya wadannan yankuna su zamo masu 'yanci, da masu cin gashin kai. La'akari da ra'ayin wakilan kasar Sin, sai aka mai da ikon samun 'yancin kai, da na kulawa da harkokin kasashen da yankunan dake karkashin kulawar sauran kasashe, ya zama daya daga cikin babban burin aiwatar da manufar sanya wasu yankuna karkashin kulawar sauran kasashe, kuma aka rubuta munufar cikin kundin tsarin aikin MDD.

Yadda wakilan kasar Sin suke nuna adalci da daidaito, ya sa suka samu amincewa daga yawancin mahalarta taron.

Bayan shawarwari da tattaunawa na tsawon watanni biyu, an zartas da kundin tsarin MDD, da kuma ka'idar kotun kasa da kasa a ran 25 ga watan Yuni na shekarar 1945. Sa'an nan kuma, a ran 26 ga watan na Yuni, cikakkun wakilai 153 daga kasashe 50 suka sanya hannu kan takardun kundin da aka rubuta da harsuna biyar, wato Sinanci, da Turanci, da yaren Rasha, da Faransanci da kuma yaran kasar Spaniya.

Dong Biwu da wasu wakilan kasar Sin ne suka sa hannu kan kundin tsarin MDD cikin hadin gwiwa, lamarin da ya nuna goyon bayan jam'iyyar kwaminis ta Sin kan kafuwar MDD. Kana, a ranar 24 ga watan Oktoba na shekarar 1945, bisa amincewar kasashen Sin, da Amurka, da Burtaniya da tarayyar Soviet da dai sauransu, kundin tsarin MDD ya fara aiki a hukunce.

Bisa kundin, baya ga kasancewarta daya daga cikin mambobin kasashen da suka kafa MDD, kasar Sin ta kuma zamo daya daga cikin kasashe masu kujerun din din din a kwamitin sulhun MDDr.

An shaida muhimmin matsayin kasar Sin a duniya ta hanyar hadin gwiwa, tare da sauran kasashe masu yaki da amfani da karfin tuwo, baya ga samun amincewa daga kasashen duniya bisa kundin tsarin mulkin MDD, musamman a lokacin da ake kara samun nasarar yaki da manufar amfani da karfin tuwo ko mulkin danniya daga dukkan fannoni.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China