in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Zhihui: Jirgin ruwa na musamman kirar Peace Ark ya shaida dadadden zumunci a tsakanin Sin da kasashen waje
2015-03-24 15:55:41 cri

A farkon shekarar 2015, aka kaddamar da aikin zaben fitattun likitoci da ke ba da taimako a kasashen waje a birnin Beijing, kuma Wang Zhihui, darektan sashen kula da harkokin ba da taimakon jinya ga kasashen waje na rundunar sojin ruwa ta kasar Sin ya zama daya daga cikin likitocin da suka ci zaben. Sau hudu ke nan ya taba zuwa wasu kasashe 18 da ke Afirka da kudu maso gabashin Asiya da kuma kudancin tekun Pasifik don gudanar da aikin ba da taimakon jinya, kuma an ba shi lambobin yabo har sau uku. Abin da ya burge malam Wang Zhihui a yayin da yake gudanar da aikin ba da taimako a kasashen waje ba wai wahalhalun da yake fuskanta ba, amma wasu jarirai hudu da aka haife su a jirgin ruwansu na Peace Ark, wadanda iyayensu suka rada musu sunayen "Peace Ark" da kuma "furen kasar Sin."

Daga shekarar 2010 zuwa ta 2014 sau hudu malam Wang Zhihui ya je kasashe 18 da ke Afirka da kudu maso gabashin Asiya da kuma kudancin tekun Pasifik don gudanar da aikin ba da taimakon jinya, inda gaba daya ya shafe tsawon kwanaki 352, tare da duba lafiyar mutanen kasashen da yawansu ya kai 72,812, kuma ya yi wa wasu 647 daga cikinsu tiyata. Malam Wang Zhihui ya ce, rundunar sojan ruwan kasar Sin da ke samar da taimako ga kasashen waje ta fi gudanar da aikinta ne a asibitin da aka gina a kan jirgin ruwa nan na musamman kirar "Peace Ark?, ya ce,

"Peace Ark da farko ya kasance wani jirgin ruwan soja, amma kuma ya bambanta da sauran jiragen ruwan soja bisa ga irin launinsa na fari fat, kuma yana da wata babbar alamar 'red cross" a jikinsa, wadda ke da matukar burgewa. Tsawon jirgin ya kai mita 178, kuma fadinsa ya kai mita 24, a yayin da tsayin jirgin ya kai mita 35.5, ma iya cewa jirgin ruwa ne babba. A yayin da jirgin ke tsayawa a tashar jiragen ruwa, ya kasance tamkar wata yarinya ce mai natsuwa, amma a yayin da yake tafiya a kan teku, zai zamanto wani mayaki. Yanzu haka kuma ya tashi a matsayin wani tauraro."

A cewar malamin, jirgin ruwan "Peace Ark" yana samun matukar farin jini a duk inda ya isa. A shekarar 2010, ya gudanar da aikin ba da taimako a kasashen waje cikin jirgin a karo na farko. A lokacin, sun gudanar da ayyuka da dama na samar da taimakon gaggawa a zangon su na farko da ke kasar Bangaladesh, inda akwai wani abun da ya faru da ba zai manta ba, ya ce,

"Har yanzu na kan tuna da wata karamar yarinya, wadda ake kiranta 'karamar China'. Abin ya faru ne a yayin da muke gudanar da aikin samar da taimako a kasashen waje cikin jirgin a shekarar 2010. A lokacin da muke kasar Bangaladesh, an yi mana kiran gaggawa cewa, akwai wata mata da ke fama da ciwon zuciya mai tsanani, sai dai ta na da ciki, kuma ta fara nakuda a lokacin da ta kai mako na 36 da junan biyun. Amma matsalar ita ce, bai kamata duk wadda ke da ciwon zuciya mai tsanani kamar ta ce ta samu ciki ba, sabo hakan zai kasance babbar barazana ga rayuwarta. A daidai lokacin, jirgin mu ya tsaya a wurin, don haka suka zo wurin mu, sai mu kuma mu duba mu yanke shawarar yi mata tiyata, sabo da mai ciwon zuciyar irin nata za ta iya mutuwa in an bar ta ta haihu ba tare da yi mata tiyata ba. A lokacin tiyata, kwararrun likitocin kula da masu ciwon zuciya da na kula da lafiyar mata da haihuwa dukkansu sun tsayawa wurin tiyata. Wata matsala ta daban ita ce a sa mata maganin hana jin zafin tiyata a jiki gaba daya ko a wani bangare kawai. Daga karshe, an sa mata maganin a bangaren jiki kawai, duk da cewa za a kara fuskantar hadari ta wannan hanya, amma hakan zai fi kyau ga lafiyar matan. Bayan tiyatar da aka yi fiye da rabin awa, an samu ciro jinjirar ba tare da matsala ba."

Amma malam Wang Zhihui bai yi zaton matan da mijinta za su rada wa wannan jaririyar sunan "China" ba, kuma likitocin kasar Sin ma sun samu babban yabo daga kafofin watsa labarai na wurin bisa ga wannan taimakon da suka bayar. Wang Zhihui ya ce,

"Mahaifin jaririyar ya yi godiya sosai, kuma nan da nan ya rada mata sunan China. Abu mai ban sha'awa shi ne a zuwanmu na biyu kasar ta Bangaladesh a shekarar 2013, iyayen sun kawo mana ziyara tare da diyarsu, kuma mun karbe su. Da suka zo jirgin, mun duba lafiyar yarinyar tare da iyayenta, abin da ya zama labari ga kafofin yada labarai na wurin, wadanda a cewarsu, karamar yarinyar nan mai suna China ta zama shaida game da zumuncin da ke tsakanin Bangaladesh da kasar China."

Malam Wang Zhihui ya ce, labarai irin nasu yarinyar suna da yawa. A cikin shekaru hudu da suka wuce, gaba daya akwai yara hudu na kasashe daban daban da aka haife su a kan jirgin ruwan Peace Ark, wadanda wasu aka yi musu sunayen "Peace Ark" ko "furen Sin", sabo da iyayensu suna so kada a manta da taimako da sauye-sauyen da jirgin ya kawo musu, tare kuma da isar da fatan alheri a game da zumunci a tsakanin kasashen su da kasar Sin, wannan kuma abu ne da ya fi faranta ran dukkanin likitocin kasar Sin da ke samar da taimako a kasashen waje, ciki har da Wang Zhihui.

An ba da labarin cewa, ma'aikatar kiwon lafiya da kayyade iyali ta kasar Sin da kungiyar sada zumunci da kasashen waje ta kasar Sin sun hada kai da sashen kula da harkokin kiwon lafiya na rundunar sojan kasar Sin wajen gudanar da wannan aiki na zabar fitattun likitocin kasar Sin da ke ba da taimako a kasashen waje, a kokarin yaba wa likitoci da kuma kungiyoyin da suka ba da babban taimako ga harkar kiwon lafiya a duniya, musamman ma likitocin kasar Sin da suke kokarin samar da taimakon yaki da cutar Ebola a kasashen waje.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China