in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lu Hongzhou
2015-03-10 14:58:38 cri

Lu Hongzhou

Namiji

Sakataren hukumar jam'iyyar kwaminis ta cibiyar kiwon lafiyar jama'a ta asibiti ta birnin Shanghai, darektan likita, kuma shehun malami.

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2014.11-yanzu

Tarihinsa: Lu Hongzhou wani kwararre ne a fannin likitanci na tawagar ba da horo kan ilmin kiwon lafiyar jama'a karon farko da kasar Sin ta turo zuwa kasar Saliyo a shekarar 2014, inda ya rike kujerar mataimakin darektan sashen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na wucin gadi na tawagar. A yayin da yake aiki a kasar Saliyo, Lu da abokan aikinsa sun yi fama da muhalli maras kyau, da ma yanayin tsaro mai cike da hadari, amma duk da haka suka yi kokari tare don gudanar da ayyukansu a yankunan dake fama da cutar Ebola. Lu ya yi amfani da ilmin da ya samu game da cututtuka masu yaduwa a asibiti, da kokarin da ya yi ne, na nuna fasahohi, da halin musamman, da kuma fifikon da kasar Sin ta samu wajen rigakafi da kuma shawo kan cututtuka masu yaduwa. Sakamakon kwarewarsa kan Turanci, Lu ya hada kai sosai tare da ma'aikatan kasar Saliyo, ta hanyoyi daban daban da suka dace ne suka ba da horo ga masu aikin jinya, masu aikin kiwon lafiyar jama'a, masu aikin gudanarwa, da kuma masu aikin jin kai na kananan sassa, kana da ba su muhimmin ilmin yaki da cutar Ebola, Lu ya kuma tsara shirin ba da horo da Turanci, ta yadda ake amfani da fasahohin da Sin ta samu na yaki da cututtuka masu yaduwa wajen yaki da cutar Ebola a wurin. Ayyukan da Lu ya gudana sun yi nasara da samun karbuwa sosai, har ma Lu ya samu babban yabo daga sassa daban daban, ciki har da shugaban kasar Saliyo da kungiyoyin kasar da kuma sauran kungiyoyin kasa da kasa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China