in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhao Chengjun
2015-03-10 10:17:46 cri

Zhao Chengjun

Namiji

Kwararren likita, kuma mataimakin daraktan sashin kula da masu fama da cututtukan zuciya, da magudanar jinni a asibitin jama'a na hudu dake birnin Jinan a lardin Shandong.

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2011.08-2013.08

Zhao Chengjun ya kammala aikinsa yadda ya kamata, na ba da agaji a ketare, aikin da ya zamo babbar nasara ga kasar Sin da ma lardin Shandong. Mr. Zhao ya kuma nuna jarumtar tawagar kasar Sin, wajen jure duk wata wahala ko kalubale, inda ya ba da gudummawa, da taimako ga masu fama da cututtuka, kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana wannan aniya, yayin ziyararsa a wasu kasashen Afirka.

A watan Agustar shekarar 2011 ne Zhao Chengjun ya isa kasar Tanzania tare da wasu abokan aikinsa, inda suka fara aikin jiyya a kasar na tsawon shekaru biyu. Baya ga gudanar da ayyukan yau da kullam, Zhao Chenjun ya kuma koyi harshen Kiswahili da kansa, har ta kai ya kan tattauna da mazauna wurin bayan watanni da dama yana koyon harshen ta hanyar zantawa da 'yan kasar.

Baya ga al'adun kasar Sin da Zhao Chengjun ya gabatar wa mazauna kasar, a daya hannun kuma ya fahimtar da su game da wasu abubuwa da suka shafi kasar Sin, wadanda ake yiwa gurguwar fahimta.

Babban aikin Mr.Zhao dai shi ne duba lafiyar masu fama da cututtuka a ko wace rana, don haka a kowace rana ya kan shiga dakunan kwantar da marasa lafiya domin duba lafiyarsu, kana a yayin da yake aiki a kasar, ya gano wasu wuraren da ya kamata ma'aikatan Tanzania su kyautata a yayin da suke aiki, don haka bisa kwarewarsa game da cututtukan zuciya, da magudanar jinni, ya ba da horo na musamman ga ma'aikatan wurin cikin shekaru biyu da suka gabata.

Gaba daya, Zhao Chengjun ya bada jawabi sau shida, yayin da kuma ya gudanar da darrusan musamman na horaswa a jami'a sau uku.

Kwarewar Zhao Chengjun kan aikinsa, ta samu amincewa, da yabo a kasar Tanzania, inda ta kai shugaban kasar ya gana da shi har sau biyu. (Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China