in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Jin
2015-03-10 09:15:53 cri

Wang Jin

Namiji

Likita mai kula da ciwon ido dake aiki a rashen kula da masu kamuwa da ciwon ido na asibiti na hudu na jami'ar koyon ilimin likitanci ta Harbin ta kasar Sin

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2009.10-2011.10, 2014.12 zuwa yanzu

Tarihinsa: Likita Wang Jin ya shiga rukunin ma'aikatan jiyya karo na shida, da lardin Hei Longjiang ya tura wa Laberiya, daga watan Oktobar shekarar 2009 zuwa watan Oktobar shekarar 2011, ya kuma kula da wadanda suka kamu da ciwon hakiya tiyata, tare da kyautata fasahar da ake amfani da ita a wannan fanni a asibitin JFK dake birnin Monrovia, hedkwatar kasar Laberiya.

Cikin wadannan lokuta, yawan tiyatar da ya yi a wannan asibiti ta kai 800, tare da sauran likitocin asitibin, adadin da ya kai matsayin koli cikin shekara daya. Ban da haka kuma, a cikin wadannan lokuta, ya yi amfani da watanni 3 ya horar da wani likita, wato Dr. Robert Dolo, yanzu haka Dr. Dolo na iya yin tiyata da kansa, kuma yawan tiyatar da ya yi cikin shekara daya ya kai fiye da 400, wanda hakan ya sanya shi zama likita da ya kai matsayin koli a yawan tiyatar ido a kasar (yanzu haka cikin kasar ta Laberiya, lititoci uku ne kacal ke iya yin irin wannan nau'i na tiyata da kansu).

Ban da haka kuma, a cikin watan Disambar bara, yayin da ake fama da cutar Ebola a yammacin Afrika, Dr Wang Jin ya maye gurbin tsohon shugaban rukunin ba da jiyya karo na 8, mai ba da taimako ga kasar Laberiya kan cutar Ebola, wanda lardin Hei Longjiang na kasar Sin ya tura, inda ya koma asibitin JFK, kuma a tsakiyar watan Disamba, ya yi tiyata ga masu ciwon hakiya karo na farko a wannan asibiti, wannan majiyaci ya warke sarai, ba tare da nuna wata alamar kamuwa da cutar Ebola ba, matakin da ya kawar da tsoron jama'a ga asibiti, kuma ya samar da zarafi mai kyau, na inganta aiki a asibiti. Daga baya kuma, yawan mutanen da suka nemi a yi musu tiyata a wannan asibiti ya karu zuwa matsayin kullum. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China