in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yu
2015-03-10 08:19:20 cri

Wang Yu

Namiji

Mataimakin darektan sashen kula da jiyyar gaggawa a asibiti na farko na birnin Yueyang da ke lardin Hunan

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: daga watan Afril na shekarar 2013

Tarihinsa:Malam Wang Yu na daya daga cikin rukunin likitocin da kasar Sin ya ta tura zuwa kasar Saliyo a karo na 16. Tun daga watan Maris na shekarar 2014, cutar Ebola ta bulla a kasashen Guinea da Liberia da ma Saliyo, kuma bisa ga yadda ofishin jakadancin kasar Sin a Saliyo ya tanadashirya, malamin ya gabatar da lacca har sau uku ga ma'aikatan ofishin jakadancin kasar Sin da na kamfanonin kasar Sin a dake kasar, don fadakar da su a kan ilmin kiwon lafiya da magance cututtuka masu yaduwa. Ban da haka, sau da dama ne ya kai rangadi tare da sauran wasu masanan na kasar Sin zuwa wasu sansanonin kamfanonin kasar Sin da ke karkarar yankunan kasar ta Saliyo, don fahimtar kimanta halin da ake ciki ta fuskar magance cutar Ebola, musamman ma bayyana matakan da ya kamata a dauka don magance cutar, da kuma rarraba magunguna da kayayyaki, ciki har da maganin kashe kwayoyin cuta, da ma abin auna zafin jiki. Ban da haka, sun kuma fadakar da ma'aikatan kamfanonin kan ilmin magance cututtukan da ake fama da su a Saliyo, ciki har da Malariya da gyambon hanta da zazzabin kwarkwata da sauransu, tare da ja hankalin al'ummar kasar Sin da ke Saliyo da su yi taka tsantsan su mai da hankali a kan rigakafin cututtuka, kuma su rika wanke hannu da kashe kwayoyin cuta, don kiwondomin kare lafiyar jikinsu. Har wa yau, sun bukaci kamfanonin kasar Sin da ke kusa da wuraren da ke fama da Ebola da su rage fitar barin ma'aikatansu na fita waje, kuma su kauracewa zuwa sassan da ke fama da cutar ta Ebola, da kuma sassan da ake samun cunkoson mutane ke cunkushejama'a, kuma in idan har dai sun suka nuna alamun kamuwa da wata cutar, misali ciwon kai da zawo da zazzabi da fitar jini, to ya kamata su gaggauta zuwa je wurin likita ba tare da jinkiri ba. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China