in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Si Haichen
2015-03-09 16:14:46 cri

Si Haichen

Namiji

Babban injiniya a sashen bincike ta X-ray, na cibiyar binciken magani, da na'urorin kiwon lafiya a babbar hukumar samar da kayayyakin soja ta kasar Sin

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2007.05-2008.02、2009.04、2010.08-2010.11、2011.09-2011.12、2013.06-2013.10

Tarihinsa: Si Haichen ya halarci asibitin Preah Ket Mealea dake kasar Cambodia, don bada gudummawa tun daga watan Mayu na shekarar 2007 zuwa watan Febrairu na shekarar 2008. Ya kuma yi aiki a asibijin sojan Taurama dake Papua New Guinea, daga ranar 3 zuwa 26 ga watan Afrilun shekarar 2009, don taimakawa wajen ajiyewa, da horar da yin amfani da na'urorin da Sin ta samar ga kasar.

Mr .Si ya kuma gudanar da aiki da jirgin ruwa na "ARK PEACE" wanda aka yi amfani da shi don gudanar da aikin kula da lafiya na "Mission Harmony 2010" a kasashe 5 na Asiya, da Afirka, tun daga ranar 20 ga watan Agusta zuwa ranar 26 ga watan Nuwanbar shekarar 2010. Har wa yau Si ya halarci kasashe 4 na Latin Amurka, don gudanar da aiki karkashin shirin na "Mission Harmony 2011", tun daga ranar 1 ga watan Satumba zuwa 29 ga watan Disambar shekarar 2011. Ya kuma kara gudanar da wani aikin dai a karkashin "Mission Harmony 2013" tun daga ranar 10 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Oktobar shekarar 2013, inda ya samar da hidimar kiwon lafiya ga sojojin dake jiragen ruwa, masu bada kariya a tekun Aden, da jama'ar dake kasashen Brunei, da Myanmar, da Cambodia, da kuma Maldives, kana ya shiga aikin bada ceto ga wadanda ke aikin su a tekun Xisha, a kan hanyarsa ta komawa gida. Don haka shugabannin ma'aikatarsa suka nuna yabo ga ayyukansa, kuma manyan hukumomi 4 na sojin kasar Sin sun ba shi lambar yabo ta "mutumin da ya fi kwazo a ayyukan taimakawa kasashen waje" a watan Disamba na shekarar 2009. (Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China