in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Huang Fan
2015-03-09 16:10:45 cri

Huang Fan

Namiji

Likitan asibitin farko na jami'ar koyon ilmin likitanci ta lardin Anhui

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2012.12-2014.01

Tarihinsa: A watan Yulin shekarar 2011 ne aka kafa jamhuriyyar kasar Sudan ta Kudu. Huang Fan ya kasance cikin rukuni na farko, na likitocin kasar Sin da aka tura zuwa kasar Sudan ta Kudu. Bayan da ya isa kasar, ya fuskanci matsaloli da dama, kamar karancin yanayin zaman lafiya, da rashin isassun na'urorin kiwon lafiya, da kuma rashin sabo da abinci, da zaman rayuwa a kasar. Amma a matsayinsa na wani likita, ya dauki alhakin bada jinya. Ya yi kokari wajen aikin kula da marasa lafiya a asibitocin dake kasar, ya kuma samu amincewa daga likitocin dake kasar. Yayin da yake aiki a asibitin Juba, ya cimma nasarori da dama a fannin ba da jinya ga mutanen da suka kamu da cututtuka masu tsanani, ta haka ne kuma ya samu yabo, da amincewa daga asibiti da ma wurin jama'ar wurin.

Ban da aiki a asibitin Juba, shi da sauran likitocin dake rukunin kasar Sin a kasar, sun shiga yankin Palouch dake Yei, da kauyen Yapa har sau uku, inda suka bada jinya ga mutane fiye da dari daya, wannan aiki ya fadada tasirin da rukunin likitocin Sin ya haifar a kasar Sudan ta Kudu. Baya ga bada jinya ga al'ummar kasar ta Sudan ta Kudu, wannan likita ya kuma bada jinya ga Sinawa dake kasar Sudan ta Kudun. Lokacin da yake daf da komowa kasar Sin, an samu barkewar rikicin zubar da jini a birnin Juba, matakin da ya sanya yawancin Sinawa dake kasar komowa gida kasar Sin, amma a nasa bangare Mr. Huang ya zauna, ya kuma ci gaba da bada jinya musamman kasancewar ana kara bukaci aikin likitoci a yayin barkewar rikici.

Haka zalika kuma, a matsayinsa na mamban rukuni na farko na likitocin Sin da aka tura zuwa Sudan ta Kudu, Huang ya tsara ka'idojin aikin rukunin, da tsarin sarrafa magani, da na'urorin kiwon lafiya da dai sauransu, matakin da ya taimakawa wajen gudanar da ayyukan rukunin da yake ciki, da harkokin zaman rayuwa na yau da kullum yadda ya kamata. Kana ya kan koyi Turanci a lokacin hutunsa, don samun saukin mu'amala da likitoci, da ma'aikata, da kuma 'yan jarida dake kasar Sudan ta Kudu cikin sauki. (Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China