in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Jinhua
2015-03-09 16:02:45 cri

Wang Jinhua

Mace

Shugabar nas ta asibiti na 2 na jami'ar koyar da ilmin likitancin soji ta 2 ta kasar Sin wadda matsayin kwarewarta ya kai darekta

Shekarun da ta yi tana aiki a waje: 2012.03-2013.03

Tarihinta: Malama Wang Jinhua ta je aikin ba da jinya a matsayinta ta shugabar tawagar kwararrun likitocin sojin da kasar Sin ta tura zuwa asibitin Preah Ket Mealea na kasar Kambodia daga watan Maris na shekarar 2012 zuwa watan Maris na shekarar 2013. Yayin da ta ke aiki a Kambodia, malama Wang Jinhua ta yi kokari matuka tare da sauran likitocin tawagarta domin horar da likitocin kasar ta hanyoyi iri daban daban saboda yanayin gudanar da harkokin asibiti da fasahar likitanci a Kambodia ba su iya biyan bukatun aiki ba, kuma babu isasshen kayayyakin kiwon lafiya da na'urorin tiyata na zamani a asibitin, har ma ba a iya yin bincike na yau da kullum yadda ya kamata. A cikin shekara daya da ta yi tana aiki a kasar, malama Wang da ma'aikatan tawagar likitocinta sun ba da jinya ga jama'ar kasar da yawansu ya kai kusan dubu goma, kuma marasa lafiya da suka kamu da cututtuka masu yaduwa ko sauran cututtuka sama da dubu daya sun warke bayan jinya da suka yi musu, ban da haka, sun samu nasarar tiyata masu wuya guda dari biyu a asibitin, alal misali, sankarar kwakwalwa, ko cire kansa, karayar kasha da ke sassan jiki da sauransu. Jama'ar Kambodia kan dauki ma'aikatan tawagar ba da jinya a matsayin gumaka wato fitattun likitoci. Ma'aikatar tsaron Kambodia ta baiwa malama Wang Jinhua "lambar yabon shimfida zaman lafiya" da "lambar yabon sada zumunta da zaman lafiya tsakanin kasashen Sin da Kambodia". (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China