in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiancheng
2015-03-09 15:24:06 cri

 Yang Jiancheng

 Namiji

 Darektan sashen fida na asibitin likitancin gargajiyar kasar Sin na birnin Changzhi na lardin Shanxi kuma likita mai matsayin mataimakin darekta

 Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2004-2006、2012.09-2014.09

 Tarihinsa: Kamar yadda mista Yang Jiancheng ya fada bayan da ya samun labarin cewa, an zabe shi a matsayin dan takarar neman zama likitoci mafi nagarta da suka ba da taimakon jinya a kasashe ketare, "Ina godiya da aikin da na yi, saboda a matsayina na likita, na fahimci yadda za a daukaka ko wane mutum cikin sahihanci. Na gode wa dukkan iyalina da abokaina, saboda sun ilmantar da ni ma'anar farin ciki da ake samu sakamakon ba da gudummowa ba tare da son kai ba. Ina godiya da irin abubuwan da suka faru a yayin da nake ba da jinya a kasar Kamaru a matsayin wani likita, lamarin da ya sa na fahimci ainihin ma'anar kauna. Yanzu ko da yake na dawo gida, amma zuciyata tana tare da kasar ta Kamaru mai nisa, wadda ita ma nake kaunarta. Kana kuma zuciyata tana tare da abokaina da ke kasar ta Kamaru, wadanda suke kaunar mu likitocin kasar Sin."

A matsayinsa na likitan fida, Yang Jiancheng bai jawo hankalin mutane sosai ba, sai bayan da wani saurayi 'dan kasar Kamaru ya yi kwanaki 12 ya tashi daga kasarsa zuwa asibitin da Yang Jiancheng yake aiki a birnin Changzhi na lardin Shanxi domin Yang Jiancheng ya ci gaba da ba shi magani a farkon shekarar 2015. Wannan saurayi da shekarunsa suka kai 38 a duniya ya gamu da karaya a kafarsa a birnin Kaifeng na lardin Henan a shekarar 2012. Nan da nan aka dora yadda ya kamata, bayan shekara guda, ya koma Kamaru da karfen da aka sa a cikin da kuma a wajen kafarsa ta yadda kafar tasa za ta warke. Amma komawarsa gida ke da wuya, sai ya gamu da matsala sakamakon kwayoyin cutar da suka shiga cikin kafar, sannan babu asibitocin da za su iya jinyar kafar tasa a Kamaru. Saboda haka wannan saurayi ya je ya ga Yang Jiancheng, wanda ya ba da taimakon jinya a kasar a wancan lokaci. Yang Jiancheng ya yi iyakacin kokarinsa na warkar da wannan saurayi duk da matsalar rashin isassun magunguna da ake fuskanta a kasar Kamaru. Bayan shekara guda, ya cire karfen da aka sa a wajen kafar wannan saurayi. Saboda babu irin wadannan karafa da suka dace a Kamaru, Yang Jiancheng bai iya cire karfen da ke cikin kafar saurayin ba. Saurayin ya ce, "To, zan je kasar Sin domin ka yi mini tiyata!"

Kamar yadda aka ambata a baya, a farkon shekarar 2015, wannan saurayi dan kasar Kamaru sai da ya kwashe kwanaki 12 kafin ya iso asibitin da Yang Jiancheng yake aiki a Changzhi, inda Yang Jiancheng ya samu nasarar cire karfen da ke cikin kafarsa. Kuma kamar yadda kungiyar likitocin kasar Sin da ke ba da taimakon jinya a kasashen Afirka ta kan yi, asibitin bai karbin kudin maganin ba. Yanzu wannan saurayi dan kasar Kamaru ya dawo gida cikin koshin lafiya.

Yang Jiancheng ya yi shekaru 34 yana aikin likitan fida. Ya taba zuwa Kamarun domin ba da taimakon jinya har sau 2, inda har kullum ya mayar da maras lafiya a gaba da kome, bai yi yawan magana ba, amma ya sauke nauyinsa na wani likita yadda ya kamata.

A ganin Yang Jiancheng, ba da taimakon jinya a kasashen Afirka, wani bangare ne na aikin sada zumunta a tsakanin kasashen Sin da Afirka. Hakika dai mutanen Afirka suna matukar bukatar taimako. Ya yi fatan zai ba su taimako gwargwadon kwarewarsa.

Yayin da ake masa magana dangane da abin da ya yi a Kamarun, Yang Jiancheng kan ce, "Ban yi kome ba. Abin da na yi, abu ne da ko wane likita kan yi. Kubutar da mutane daga bakin mutuwa, nauyi ne da aka dora mini."(Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China