in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Zhihui
2015-03-09 14:39:36 cri

Wang Zhihui

Namiji

Likita mai matsayin darekta, kuma shugaban sashen tsara shirye-shirye na ma'aikatar kiwon lafiya ta sojojin ruwa na kasar Sin

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2010-2014

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: Daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2014, Wang Zhihui ya taba zuwa kasashe 18 da ke nahiyar Afirka, kudu maso gabashin Asiya, da kuma kudancin tekun Pasific don gudanar da ayyukan ba da jinya na jin kai cikin jirgin ruwa na musamman kirar "Peace Ark" na sojojin ruwan kasar Sin domin lura da marasa lafiya. A cikin aikinsa na sau hudu, wanda ya shafi kwanaki 352 da kilomita dubu 110, Li Zhihui ya ba da taimako wajen ba da jinya ga mutanen kasashen waje kimanin 72812, tare da yin tiyata 647. Hakan ya sa ya samu amincewa da babban yabo daga shugabanni da kuma likitoci bisa babbar gudummawar da ya bayar.

Ya zuwa yanzu dai, kasar Sin ta shirya aikin ba da jinya sau biyar gaba daya a ketare cikin jirgin ruwa na musamman, likita Wang kuma ya sa hannu a cikin hudu daga cikinsu, hakan ya ba shi zarafin zama mai jagora ga wannan aikin ba da taimakon jinya a kasashen waje.

Jirgin ruwa na musamman na kasar Sin da ke ba da kulawa ga marasa lafiya ya kawo muhimmin tasiri wajen ci gaban aikin diplomasiyya ta fuskar soja, inda likita Wang Zhihui ya ba da babban taimakonsa wajen daga martabar aikin a kasashen duniya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China