in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Me ya sa aka shirya Bikin ba da lambar yabo ga fitattun likitocin da ke ba da taimako a kasashen waje na shekarar 2015
2015-03-09 14:17:34 cri

Tun lokacin da kasar Sin ta fara tura likitocinta na ba da taimako zuwa kasar Aljeriya a shekarar 1963, kasar Sin ta kwashe shekaru 52 tana wannan aiki. A shekarar ta 2013, a lokacin da yake ganawa da fitattun kungiyoyin ba da taimakon jinya da likitoci wadanda suka ba da taimakon jinya a ketare, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, ba da taimakon jinya a kasashen waje ya kasance wani muhimmin abu ne a cikin harkokin waje da kasar Sin ke aiwatarwa. Dimbin likitoci sun ba da gudummawa matuka ga wannan aiki. Ba ma kawai sun ciyar da harkokin kiwon lafiya na kasashen da suka samu irin wannan taimakon jinya gaba bisa nagartattun fasahohinsu na ba da jinya da da'a ba, har ma sun bayyana yadda Sinawa suke kishin zaman lafiya da girmama rayuka. Bugu da kari, sun zama wakilan jama'a na sada zumunta a tsakanin al'ummar kasar Sin da ta kasashe wadanda suka samu irin wannan taimakon jinya.
A watan Faburairu na shekara ta 2014, annobar Ebola ta barke sosai a yankin yammacin Afirka. A gaban wannan rikicin kiwon lafiyar jama'a, nan da nan gwamnatin kasar Sin da rundunar sojanta sun tashi sun tura rukunonin kwararrun likitoci kusan sau 10 zuwa kasashen yammacin Afirka, inda suka kunshi likitoci da sauran ma'aikatan aikin jinya fiye da dubu 1. Sakamakon haka, kasar Sin ta samu yabo sosai daga wajen kasashen Afirka da al'ummominsu da sauran kasashen duniya.
Kwamitin kiwon lafiya da tsara shirin haihuwa na kasar Sin da kungiyar sada zumunta tsakanin al'ummar kasar Sin da ta kasashen duniya sun shirya wannan "bikin ba da lambar yabo ga fitattun likitocin da ke ba da taimako a kasashen waje na shekarar 2015", ta yadda za a iya jawo hankulan jama'a da su mai da hankali kan aikin ba da taimakon jinya a ketare, kuma za su iya kulawa da nuna goyon baya ga wadannan likitocin ba da taimakon jinya a kasashen waje wadanda ba a san sunayensu ba.


Wadanda suka shirya bikin:  Hukumar kiwon lafiya da tsara iyali ta kasar Sin da Kungiyar sada zumunta a tsakanin jama'ar kasar Sin da na kasashen ketare
Wanda ya goyi bayan shirya bikin: Sashen kiwon lafiya na ma'aikatar kula da harkokin samar da kayayyaki ta rundunar sojan kasar Sin
Wanda ya ba da taimako wajen shirya bikin: Asusun sada zumunci da wanzar da zaman lafiya da ci gaba na kasar Sin
Kafar yada labaru da ta taimaka wajen shirya bikin: Gidan rediyon kasar Sin CRI   (Sanusi Chen & Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China