in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhang Depeng
2015-03-09 13:57:42 cri

 Zhang Depeng

 Namiji

 Darektan sashen daukar hoton sassan jikin dan Adam (X-ray) na asibitin rundunar soja ta 8 da ke yankin Tibet, wanda kwarewar aikinsa ta kai mataki na 5

 Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2004.08-2006.02

 Tarihinsa: A watan Agusta na shekarar 2004, mista Zhang Depeng ya jagoranci wata tawagar likitoci zuwa kasar Ecuador inda suka kwashe shekara daya da rabi suna bayar da tallafin aikin jinya.

A yayin da yake gudanar da aikin, Zhang Depeng ya yi kokarin daukaka matsayin kasar Sin a idanun al'ummar kasar Ecuador, da karfafa dankon zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen 2, inda ya yi amfani da kwarewarsa wajen jinyar wasu mutanen da suka kamu da cututtuka masu tsanani, abin da ya sanya jama'ar kasar Ecuador suka yaba masa har ma suka yi imani da shi.

Duk da cewa kasar Ecuador tana fama da matsalar rashin muhimman abubuwan da ake bukata domin gudanar da aikin likitanci, amma Zhang Depeng da abokan aikinsa ba su damu da wannan ba, inda suka koyar da likitocin kasar Ecuador tunani da fasahohin ci gaba a fannin aikin likitanci.

Zhang ya kwashe shekaru fiye da 30 yana aiki a matsayin likita, saboda haka ya kware sosai a fannin daukar hoton sassan jikin dan Adam (X-ray), har ila yau, ya samu nasarori sosai a fannin amfani da allurar gargajiyar kasar Sin da fasahar murmure jiki don jinyar mutanen da ke fama da rashin lafiya, wanda ya riga ya rubuta rahoton bincike kusan dari 1 a wadannan fannoni.

Bisa kwarewar da ya samu a fannin yin amfani da allurar gargajiyar kasar Sin da fasahar murmure jiki, Zhang ya yi kokarin yayata fasahohin gargajiyar kasar Sin ta fuskar aikin jinya tsakanin jama'ar kasar Ecuador, a yayin da yake aikin sa-kai a kasar, lamarin da ya sa ya samu yabo sosai. Kana ma'aikatar tsaron kasar Ecuador ta ba shi wata lambar yabo ta "tauraron sojoji" don nuna masa girmamawa kan kyawawan halayyarsa da nasarorin da ya cimma a fannin aikin jinya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China