in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
He Xiangwu
2015-03-09 13:55:27 cri

 He Xiangwu

 Namiji

 Darektan sashen kula da ayyukan ba da jinya na asibitin rundunar soja ta 91 da ke yankin Jinan, kuma likita mai matsayin mataimakin darekta

 Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 1996.01-1996.12、2006.01-2006.12

 Tarihinsa: He Xiangwu ya taba yin aikin jinya a asibitocin kasar Cuba a shekarar 1996 da kuma 2006. Ya shafe tsawon watanni 36 yana aiki a ketare. Yayin da yake ba da taimakon jinya a kasar Cuba, He Xiangwu ya duba marasa lafiya fiye da dubu 2 baki daya da ke jinya a asibiti. Sa'an nan kuma a lokacin hutunsa, ya yi aikin sa-kai inda ya duba marasa lafiya a unguwar Sinawa 'yan kaka gida har sau 37.

Ko da yake ana fuskantar kuncin zaman rayuwa a kasar Cuba, sannan kuma ana fuskantar matsaloli wajen gudanar da ayyukan jinya, saboda rashin kayayyakin kiwon lafiya masu inganci. Bayan haka kuma ga cututtuka masu yaduwa da dama, kamar gyambon hanta nau'in A, zazzabin Dengue, cututtukan hanta da kwari ke haddasa wa da dai sauransu kan yadu cikin sauri kasancewar kasar ta Cuba na yankin da ke fama zafi. He Xiangwu, a matsayinsa na likita, yana fuskantar barazanar kamuwa da cututtukan a ko da yaushe, amma bai taba ja da baya ko kadan ba yayin da yake fuskantar wahalhalu da kuma duba majiyyata. A ko da yaushe He Xiangwu kan nuna himma sosai wajen gudanar da ayyukan jinya, ya sauke nauyinsa yadda ya kamata a matsayinsa na sojan kasar Sin, kuma wani likita na kasar Sin.

A lokacin da yake gudanar da aikin jinya a kasar Cuba, baya ga sa himma wajen ba da jinya da kuma ilmantar da mazauna wurin kan bayanan kiwon lafiya, He Xiangwu ya koyar da marasa lafiya da kuma mazauna wurin wasan karate na Tai Chi, a kokarin yayata al'adun gargajiyar kasar Sin ta fuskar motsa jiki. Bisa gayyatar da gidan telibijin na kasar Cuba ya yi masa, He Xiangwu ya ba da taimako wajen tsara shirin telibijin na musamman kan yayata wasan Tai Chi, wanda ya sanya dimbin mazauna wurin koyon wasan na Tai Chi.

He Xiangwu ya samu lambobin yabo na "sada zumunta da wanzar da zaman lafiya" da na "sada zumunta a matsayin soja mai nagarta" daga wajen shugaban kasar Cuba sakamakon wadannan gudummowa da ya bayar a kasar. A shekarar 2009 kuma hedkwatar kwamitin tsakiya ta rundunar sojan kasar Sin ta zabe shi a matsayin soja mai nagarta ta fuskar gudanar da aikin taimako a ketare, har wa yau kuma, rundunar ta ba shi lambobin yabo da dama. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China