in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Lijun
2015-03-09 13:53:53 cri

Wang Lijun

Maza

Likita ne a matsayin mataimakin darekta na babban asibitin jami'ar koyon ilmin likitanci ta Birnin Tianjin, kuma dan tawagar ba da jiyya ta kasar Sin da ke ba da taimako a Jamhuriyar kasar Kongo

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2013.07 zuwa yanzu

Tarihinsa: Wang Lijun, wani likita ne a sashen ba da jiyyar gaggawa da ke babban asibitin jami'ar koyon ilmin likitanci ta birnin Tianjin. A watan Juli na shekarar 2013, ya tashi zuwa Jamhuriyar kasar Kongo wato Kongo Brazzaville don kaddamar da aikinsa na ba da taimakon jinya, kuma har yanzu yana aiki a wannan kasa.

Sakamakon yanayin zaman rayuwa maras kyau, da kuma mummunan sharadin ba da jinya bisa karancin magunguna da kayayyakin masarufi, ba yadda za a yi dai Wang Lijun ya gudanar da aikinsa bisa halin da ake ciki a asibitin sada zumunci tsakanin Kongo Brazzaville da Sin, amma duk da haka ya kubutar da mutane kusan 100 masu kamuwa da cututtuka masu tsanani, ciki har da wani da ya kamu da cutar dake haifar da saurin bugun zuciya, da wani da ya kamu da cutar malariya mai raunata sassan kwakwalwa, wanda ya kasance mutumin farko da asibitin ya karba da ya kamu da irin wannan cutar.

Ban da gudanar da aikin ba da jinya na yau da kullum, likita Wang ya horar da likitocin kasar kan yadda ya kamata a zira bututun iska cikin makogwaro, da yadda ya kamata a yi amfani da na'urar taimakawa numfashi, gami da fasahar sauraron sautuka da suka zarce ji irin na bil Adama da ake amfani da ita a ayyukan likitanci, hakan ya kyautata kwarewar likitocin wurin wajen amfani da na'urorin zamani na jinya.

Bayan abkuwar cutar Ebola mai saurin kisa a kasashen Afirka, likita Wang da abokan aikinsa sun yi iyakacin kokarinsu wajen shawo kan cutar.

Ya zuwa watan Janairu na shekarar 2015, likita Wang Lijun ya ba da jinya ga mazauna wurin 3200 marasa lafiya da ba a kwantar da su ba a asibiti, kana da wadanda aka kwantar da su a asibiti kusan 100. Kuma ya yi wa mazauna wurin 1300 bincike bisa fasahar sauraron sautuka da suka zarce ji irin na bil Adama. Har ma ya ba da laccoci fiye da 10 ga likitocin wurin. Hakan ya sa ya samu karbuwa sosai daga mazauna wurin bisa gudummawar da ya bayar ga aikin jinya na Jamhuriyar kasar Kongo.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China