in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guo Liang
2015-03-09 13:49:32 cri

Guo Liang

Namiji

Mataimakin shugaban asibitin kulawa da cutar Cancer dake lardin Zhejiang, kana likita mai lura da masu jiyyar cutar Cancer dake matsayin darekta, kana shugaban rukunin likitanci da Sin ta tura zuwa Mali karo na 23.

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2013.07 zuwa yanzu

Tarihinsa: Mali kasa ce dake yammacin Afirka, tana kuma sahun baya a fannin tattalin arziki da aikin likita, wuri ne da cututtuka da dama su kan yadu. Mista Guo Liang ya sauke nauyin dake wuyansa, na taimakawa sauran kasashen duniya, halayensa na da kirki, da kuma girmamawa, da kulawa ga wadanda suka kamu da cututtuka na kasar ta Mali ya sanya shi samun karbuwa matuka.

 Mista Guo ya taba lura da wasu mutane biyu masu dauke da kwayoyin cutar AIDS, ya kuma ci nasarar aiki a kan su. Dadin dadawa, ya kasance yana gudanar da aiki a lokacin hutu, domin biyan bukatun marasa lafiya.

A matsayinsa na ja-gora a reshensa, mista Guo ya jagoranci rukunin likitanci waje wajen nazarta sabbin fasahohi da sarrafa su, ciki har da fannonin da a baya, ba a taba samun su a kasar ta Mali ba.

A sakamakon kyakkyawan aikin da rukunin mista Guo ya yi, manyan jaridun kasar Mali sun rubuta labarai dangane da shi har karo 8, yayin da tasoshin yanar gizo suka ba da labarin irin himmarsa har sau biyu, kana gidan talibijin na kasar Mali ya gabatar da labarinsa sau biyu, hakan ya daga matsayin rukunin likitocin Sin a kasar ta Mali.

Mista Guo Liang da sauran mambobin rukunin sun ba da jiyya, da kula ga firaministan kasar Mali, da babban shugaban hukumar kididdigar kasar, da sauran manyan jami'an kasar Mali.

Bisa jagorancinsa da kokarin kowa da kowa, an bude cibiyar ba da jiyyar cutar Cancer, irin ta tilo a kasar ta Mali. Hakan ya sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin kiwon lafiya a kasar Mali kwarai da gaske.

Ban da haka, kasar Mali, wuri ne da aka samu bullar cutar Ebola. Don haka Mista Guo ya ci gaba da aikinsa a wurin tare da sauran membobin rukunin. A karshe kuma sun cimma burinsu na "Yaki da cutar Ebola ba tare da kamuwa da ita ba". (Fatima Liu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China