in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xu Xun
2015-03-09 13:47:40 cri

 Xu Xun

 Namiji

 Likita dake matsayin mataimakin darekta mai aiki a asibitin jama'a na birnin Jiangyou dake lardin Sichuan

 Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2014.10-2015.01

 Tarihinsa: A shekarar 2014, a kokarin ba da gudummawa ga sha'anin ba da jiyya na kasa da kasa, Xu Xun ya bukaci shiga aikin bada tallafin kwararru a ketare bisa radin kansa. A ranar 31 ga watan Oktobar bara, mista Xu ya kai ziyara kasar Mozambique tare da sauran membobin tawagar likitocin lardin Sichuan.

Xu Xun yana matukar darajanta wannan zarafi na aiki a ketare. Baya ga fatan fidda jama'ar kasashen Afirka daga wahalhalu, Xu yana da kuma burin fadada kwarewarsa, da kara bude ido a fannin likitanci na duniya. Dadin dadawa, kwarewarsa da hakurinsa sun sa ya samu yabo, da girmamawa daga abokan aikinsa, da kuma jama'ar kasashen Afirka, har ma akan yi masa kirari da "Managarcin likita" a birnin Maputo, hedkwatar kasar Mozambique.

A cikin ayyukansa na yau da kullum kuma, mista Xu ya kan taimakawa mutane a wurare daban daban. Wata rana, wani mutum da matarsa suna shakatawa a bakin teku tare da yaronsu da bai wuce shekara daya ba. Ba zato ba tsammani, ruwan teku ya kwace wannan yaro. A daidai wannan lokaci, Xu Xun ya lura da abin da ke faruwa, kuma nan take ya yi kundumbala cikin tekun ya kuma ceci ran wannan yaro. Iyayen wannan yaro sun yi matukar godiya ga mista Xu bisa wannan taimako da ya yi musu. Wannan shi ne tunani irin na jin kai da Xu ke da shi.

A sakamakon yawan shan aiki, da kuma rashin sabo da cin abinci da yanayin ketare, a yammacin ranar 24 ga watan Janairun bana, da misalin karfe 7 da minti 15, yayin da yake aikin ba da jiyya, Xu Xun ya rasu sakamakon ciwon zuciya. Xu ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 50 da haihuwa kawai. Yayin bikin ban kwana da gawarsa, mataimakin ministan kiwon lafiya na Mozambique ya bayyana cewa, "A wannan lokaci na alhini, mun yi amanna da duk gudummawar da ka bayar, ka taimakawa jama'ar kasar mu wajen shawo kan cututtuka, da rage wahalhalunmu."

Mista Xu ya sadaukar da ransa ga sha'anin ba da taimakon jinya ga kasashen waje, ya sami babban yabo, da girmamawa daga kasashe, da jama'ar da suka sami taimakonsa. (Fatima Liu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China