in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Zhenchang
2015-03-09 10:14:44 cri

Wang Zhenchang

Namiji

Mataimakin shugaban asibitin zumunta dake karkashin jami'ar horar da likitoci ta "Capital" dake nan Beijing na kasar Sin, likita dake matsayi na dirakta, shehun malamin dake koyar da dalibai masu neman digiri na uku, shugaban tawagar rukuni na 24 na ma'aikatan jiyya da kasar Sin ta tura zuwa kasar Guinea.

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: tun daga watan Agusta na shekarar 2014 zuwa yanzu.

Tarihinsa: A matsayinsa na shugaban tawagar ma'aikatan jiyya rukuni na 24, wanda kasar Sin ta aika zuwa kasar Guinea, Wang Zhenchang ya jagoranci wannan tawaga zuwa kasar Guinea a kan lokaci, inda suka kammala sauyin aiki da tawagar rukuni na 23 cikin nasara, a lokacin da ake tsaka da fama da yaduwar cutar Ebola a kasar.

Sakamakon hadin gwiwar da Mr. Wang ya yi tare da hukumar kiwon lafiya ta kasar Guinea, da asibitin Zumunta na Sin dake Guinea, an shigar da na'urori na zamani na kasar Sin zuwa asibitin Zumunta na Sin dake Guinea, matakin da ya ba da damar inganta ayyukan jiyya a asibitin, haka kuma, Mr. Wang ya yi amfani da fasahohi na masana a fannin aikin jiyya na Sin, wajen kafa wata cibiyar ba da agaji ta kasa da kasa a asitibin Zumuntar, inda aka cimma nasarar horas da karin lokitoci a kasar, lamarin da ya samu yabo, da goyon baya matuka daga hukumar kiwon lafiyar kasar, da kuma shugaban asibitin.

Tun dai barkewar cutar Ebola a wasu kasashen yammacin Afirka, gwamnatin kasar Sin ta aike da tawagogin masana har sau hudu, zuwa kasar ta Guinea domin taimakawa Sinawan dake kasar wajen kare kansu daga kamuwa da cutar. Haka kuma a matsayinsa na shugaban tawagar masana masu ba da horo, Wang Zhenchang ya yi matukar baiwa aikin tawagar gudummawa, bisa jagorantarsa an cimma nasarar kammala aikin ba da horaswa ga mazaunan kasar kimanin dubu 2, game da dabarun kandagarkin kamuwa da cutar ta Ebola. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China