in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu muhimman takardun da aka fitar bayan cikakken zama karo na 3 na kwamitin tsakiya na JKS na 18
2014-11-11 15:47:30 cri
1. Wasu ra'ayoyin kara yin kwaskwarima a kauyuka daga dukkan fannoni da hanzarta zamanintar da aikin gona (Kwamitin tsakiya na JKS da majalisar gudanarwa ta kasar Sin sun fitar da su ne a ran 2 ga watan Janairu na shekarar 2014.)

2. Kudurin soke wasu dokokin neman izini daga hukumomin gwamnati da sakarwa gwamnatocin gundumomi da kananan hukumomi mara na tafiyar da harkokinsu (majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta fitar da shi ne a ran 14 ga watan Faburairu na shekarar 2014.)

3. Shirin yin kwaskwarima ga ka'idojin yin rajista a harkar zuba jari (majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta fitar da shi ne a ran 17 ga watan Faburairu na shekarar 2014.)

4. Tunanin bullo da tsarin inshori na bai daya ga tsoffi mazauna birane da manoma (majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta fitar da wannan takarda ce a ran 24 ga watan Faburairu na shekarar 2014.)

5. Babban shirin yin kwaskwarima ga tsari da biyan kudin haraji (an tattauna wannan shiri ne a yayin taro karo na 3 na rukunin shugabannin kula da aikin karfafa yin kwaskwarima na kwamitin tsakiya na JKS a ran 6 ga watan Yuni na shekarar 2014, sannan aka fitar da shi a ran 30 ga watan Yuni.)

6. "Ra'ayoyin yin kwaskwarima ga ka'idojin yin amfani da motocin gwamnati baki daya" da "shirin yin kwaskwarima ga ka'idojin yin amfani da motocin hukumomin kwamitin tsakiya na JKS da na gwamnatin tsakiya" (An fitar da su ne a watan Yuli na shekarar 2014)

7. "Shirin yin kwaskwarima ga tsarin albashi da kudin alawus ga ma'aikatan masana'antu da kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiya" da "Ra'ayoyin daidaita tsarin albashin ma'aikatan masana'antun mallakar gwamnati da kudin da ya kamata su kashe lokacin da aka tura su wani wuri aiki" (An nazarci wadannan batutuwa a yayin taro karo na 4 na rukunin shugabannin kula da aikin yin kwaskwarima na kwamitin tsakiya na JKS a ran 18 ga watan Agusta na shekarar 2014)

8. "Ra'ayoyi kan yadda manoma suke da ikon ba da hayar gonakinsu bisa doka, da kuma bunkasa aikin gona ta hanyar da ta dace" da "shirin gwaji na yin kwaskwarimar sa kaimi kan hade hannayen jari na manoma waje guda da amincewa da mayar da dukiyoyin kauyuka su zama hannun jari" (An nazarci wadannan batutuwa yayin taro karo na 5 na rukunin shugabannin kula da aikin karfafa yin kwaskwarima na kwamitin tsakiya na JKS a ran 29 ga watan Satumba na shekarar 2014, kana aka fitar da su a yayin taron kwamitin tsakiya na JKS na watan Oktoba.)

9. Shirin kara yin kwaskwarimar sa ido kan yadda ake amfani da kasafin kudi na gwamnati (da kudin da aka kebe wa wani shiri musamman ko kudin da aka samu daga wani asusu) a fannonin kimiyya da fasaha (An duba su a yayin taro karo na 5 na rukunin shugabannin kula da aikin karfafa yin kwaskwarima na kwamitin tsakiya na JKS a ran 29 ga watan Satumba na shekarar 2014, kuma an fitar da su a yayin taron kwamitin tsakiya na JKS na watan Oktoba.)

10. Kudurin kara yin kwaskwarima ga tsarin yin amfani da kasafin kudi (majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta fitar da shi a ran 9 ga watan Oktoba na shekarar 2014.)

11. Ra'ayoyin shimfida da gabatar da sakamakon da aka samu yayin da ake gwajin raya yankin yin cinikayya cikin 'yanci na kasar Sin dake Shanghai na gwaji (An duba su a yayin taro karo na 6 na rukunin shugabannin kula da aikin karfafa yin kwaskwarima na kwamitin tsakiya na JKS a ran 27 ga watan Oktoba na shekarar 2014, kuma an fitar da su a ran 6 ga watan Nuwamba a yayin taron kwamitin tsakiya na JKS.)

12. Ra'ayin daidaita da kuma kyautata manufofin da suka shafi batun haihuwa (kwamitin tsakiya na JKS da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ne suka fitar da shi a ran 25 ga watan Disamba na shekarar 2013)

13. "Shirin aiwatar da aikin kara yin kwaskwarima ga tsarin bunkasa al'adu" (An duba da kuma fitar da shi a yayin taro karo na 2 na rukunin shugabannin kula da aikin karfafa yin kwaskwarima na kwamitin tsakiya na JKS a ran 28 ga watan Faburairu na shekarar 2014)

14. "Ra'ayoyi kan wasu matsalolin da suka kunno kai yayin da ake yin kwaskwarimar ga tsarin shari'a" da "shirin yin kwaskwarima na gwaji kan tsarin shari'a na birnin Shanghai" da "shirin kafa kotun kare ikon mallakar fasaha" (An duba da kuma gabatar da wadannan ne a yayin taro karo na 3 na rukunin shugabannin kula da aikin karfafa yin kwaskwarima na kwamitin tsakiya na JKS a ran 6 ga watan Yuni na shekarar 2014)

15. Shirin yin kwaskwarima ga tsarin ladabtarwa da bincike na JKS (An duba da kuma fitar da shi a ran 30 ga watan Yuni na shekarar 2014)

16. Ra'ayoyin kula da aikin hada kan kafofin yada labaru na gargajiya da kafofin yada labaru na zamani (An duba da kuma fitar da shi a yayin taro karo na 4 na rukunin shugabannin kula da aikin karfafa yin kwaskwarima na kwamitin tsakiya na JKS a ran 18 ga watan Agusta na shekarar 2014.)

17. Ra'ayoyin aiwatar da aikin kara yin kwaskwarima ga ka'idojin jarrabawa da daukar daliban jami'o'i (An duba da kuma fitar da shi a yayin taro karo na 4 na rukunin shugabannin kula da aikin karfafa yin kwaskwarima na kwamitin tsakiya na JKS a ran 18 ga watan Agusta na shekarar 2014.)

18. Shirin aiwatar da aikin yin kwaskwarima ga tsarin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, JKS (An duba da kuma zartas da shi a yayin taron hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS a karshen watan Agusta na shekarar 2014)  (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China