in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaru daga jaridun Afirka
2010-01-08 15:50:31 cri

A cikin shirinmu na yau, bari mu fara duba wani labari da muka samu daga jaridar the New Times ta kasar Ruwanda, wadda aka buga a ran 7 ga wata, inda aka bayyana cewa, kasashen Ruwanda da Burundi za su kara hada kansu domin yaki da laifuffukan da ake gudanarwa a bakin iyakokin kasashen biyu.

A ran 6 ga wata, shugabannin 'yan sanda na kasashen Ruwanda da Burundi sun shirya wani taro na kwana guda domin nuna aniyarsu wajen yaki da laifuffukan da ake gudanarwa a bakin iyakokin kasashen biyu.

A gun taron, an fi mai da hankali kan hadin kai a tsakaninsu bisa tushen takardar fahimtar juna da suka daddale a watan Afrilu na shekarar 2009, inda shugabannin 'yan sanda na Ruwanda da Burundi suka sa hannu a kai.

A yayin da yake zantawa da wakilin jaridar The New Times, kakakin 'yan sanda na kasar Ruwanda mista Eric Kayiranga ya bayyana cewa, wannan taro ya shaida cewa, ko wace kasa, Ruwanda da Burundi ba kaiwai za ta yaki da laifuffukan da ake gudanarwa a gida ba, har ma za su kara hada kansu domin kara yaki da laifuffuka a bakin iyakokin kasashen biyu.

Bisa shirin da aka tsara, an ce, bangarorin biyu na hukumomin kiyaye zaman lafiya na kasashen biyu sun dauki niyyar shirya tarurruka a duk tsawon kowane watanni 6.

Laifuffukan da suka sa hannu kansu wajen yin hadin gwiwa a bakin iyaka sun hada da satar motoci, da daukar makamai ba bisa doka ba, da kuma yin jigilar miyagun kwayoyi, da sayar da kudaden jabu.

Kakaki Kayiranga ya ce, game da aikin yaki da satar motoci, wannan taro ya sanar da cewa, kasashen biyu za su more labarun da suka samu. Ban da wannan kuma, kasashen biyu za su hada kansu wajen yaki da laifuffukan da ake gudanarwa dangane da muhalli, wadanda suke zama sababbin sunayen laifuffuka da aka amince da su.

Shugaban 'yan sanda na kasar Burundi mista Fabien Ndayishimye ya ce, wannan taro zai kara sa kaimi ga hadin kai a tsakanin kasashen biyu. Ya ce,

'Tarurruka kamar haka suna iya sa kaimi ga hadin kai a tsakaninmu. Mun yi alkawarin cewa, za mu aiwatar da ra'ayin da aka samu a wannan taro nan da nan.'

Jama'a masu karatu, bayan haka kuma, bari mu sake duba wani labari da muka samu daga shafin internet na Times Of Zambia, wanda aka buga a ran 7 ga wata, inda shugaban kasar Zambia mista Rupiah Banda ya yi kira ga jama'ar Zambia da su yi rajista, kuma ya yi kira ga shugabannin jam'iyyun siyasa da ke adawa da gwamnati da su yi rajista domin shirya sosai ga babban zabe da za a gudanar a shekarar 2011.

Shugaba Banda ya ce, ya fi kyau shugabannin jam'iyyun siyasa da ke adawa da gwamnati su sa kaimi ga jama'arsu da su yi rajista wajen jefa kuri'a, kada su tattauna kan gurbin aiki na shugaban kasa kawai ba.

A ran 6 ga wata, shugaba Banda ya yi wannan kira ga jama'a da su yi rajista su zama masu kada kuri'a a babban zaben da za a gudanar a shekarar 2011. Ya ce,

'Na yi kira ga ko wace jama'a da ta san cewa, za a gudanar da zabubuka a shekarar 2011, haka kuma kwamitin da ke kula da harkokin zabe ya riga ya shirya yadda ya kamata. Ina so in yi kira ga dukkan jama'ar Zambia da su yi rajista su zama masu kada kuri'a.'

Ya kara da cewa, ya kamata shugabannin siyasa su yi kira ga jama'arsu da su yi rajista, kada su tattauna kan gurbin aiki na shugaban kasa kawai, ya kamata su amince da cewa, jama'arsu sun yi rajista.

Ya ce, idan yawancin jama'a sun yi rajista sun zama masu kada kuri'a, to, wannan ya bayyana cewa, jama'a za su shiga cikin aikin zaben shugabannnin kasar a nan gaba.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China