logo

HAUSA

A Karo Na Farko Yawan Wutar Lantarki Da Kasar Sin Ta Samar Ta Hanyar Amfani da Sabbin Makamashi A Shekara Guda Ya Zarce Kilowatt-hours Triliyan 1

2021-12-27 13:54:58 CRI

A Karo Na Farko Yawan Wutar Lantarki Da Kasar Sin Ta Samar Ta Hanyar Amfani da Sabbin Makamashi A Shekara Guda Ya Zarce Kilowatt-hours Triliyan 1_fororder_NEW

Alkaluman da hukumar kula da makamashin kasar Sin ta gabatar a kwanakin baya, sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa na Nuwamban shekarar da muke ciki, yawan wutar lantarki da kasar Sin ta samar ta hanyar amfani da sabbin makamashi ya kai Kilowatt-hours biliyan 1035.57, inda a karo na farko adadin ya wuce Kilowatt-hours triliyan 1, wanda ya karu da kaso 32.97 cikin dari, bisa makamancin lokaci na shekarar bara, kuma ya kai kashi 13.8 cikin dari bisa jimillar yawan wutar lantarki da ake amfani da ita a duk fadin kasar Sin, daga watan Janairu zuwa na Nuwamban shekarar da muke ciki, inda ya karu da kashi 2.14 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar bara.

Kaza lika adadin ya kai kwatankwacin yawan wutar lantarki da aka yi amfani da shi a biranen kasar baki daya. Sabbin makamashi suna rika, suna kuma ba da gudummowa wajen samar da wutar lantarki a kasar Sin. Aikin samar da wuta ta hanyar amfani da sabbin makamashi ya samu saurin ci gaba a kasar Sin.

Har ila yau, kasar Sin ta kyautata karfinta na samar da wutar lantarki ta hanyoyin hasken rana, da ruwa, da makamashin nukiliya, da karfin iskar teku.

Tasallah Yuan